Wani mutumi ya yiwa matarsa askin kwal-kwabo saboda ya tsinci gashi a abincinsa

Wani mutumi ya yiwa matarsa askin kwal-kwabo saboda ya tsinci gashi a abincinsa

Rundunar yan sandan Bangladesh a ranar Talata ta bayyana cewa an kana mutumin kasar, wanda ya yiwa matarsa aski ta karfin tsiya bayan ya tsinci gashi a cikin abincinsa na safe.

Kamar yadda ya zo kungiyoyin kare hakkin jama’a sun yi gargadin cewa ana samun hauhawan yawan cinzarafin mata a kasar ta Musulunci.

Yan sanda sun kai mamaya wani kauye a yankin arewa maso yammacin Joypurhat sannan suka kama Bablu Mondal mai shekara 35 bayan mazauna kauyen sun sanar da jami’an batun lamarin.

“Ya tsinci gashin mutum akan shinkafa da madarar da matarsa ta shirya masa na karin kummalo,” Shugaban yan sandan yankin Cif Shahriah Khan ya sanar da AFP.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun gurfanar da magidanci akan cin zarafin matarsa

“Sai ya fusata a lokacin da ya ga gashin sannan ya daura laifin akan matar. Daga nan sai ya dauki reza ya aske gashin kan matar tasa,” inji shi.

Khan yace ana tuhumar Bablu da haifar da radadin zuciya, laifin da ke dauke da hukuncin shekara 14 a gidan yari.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari, ta yi kira ga muhukunta da kuma masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar mataki a kan yadda malamai ke keta haddin dalibai mata a jami'o'i da makarantun gaba da sakandire na kasar.

Hajiya Aisha ta yi kiran ne a daren ranar Litinin da ta gabata yayin halartar wani shiri da kafar watsa labarai ta BBC Hausa ta yi dangane da yadda malaman makarantun gaba da Sakandire a Najeriya ke lalata da dalibai 'yan mata domin ba su maki a jarrabawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel