Pantami da shugaban NITDA sun kirkiri wata muhimmiyar na'ura

Pantami da shugaban NITDA sun kirkiri wata muhimmiyar na'ura

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani ta Najeriya (NITDA) a ranar Litinin a taron baje kollin na fasaha (GITEX) da ke gudanarwa a Dubai ta saka Najeriya cikin jerin sunayen kasashen da suka kware wurin fasaha ta hanyar kaddamar da wata na'ura da ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami da direktan NITDA, Dakta Agu Collins Agu suka kirkira.

Na'urar da aka tsara kuma aka kirkira cikin shekaru biyu zai iya koyar da yara na makarantun firamare ilimin na'ura na wucin gadi (Artificial Intelligence) da fasahar sadarwa na bayanai na musamman (Internet of Things) kamar yadda Agu ya shaidawa Daily Trust a hirar da su kayi a Dubai a ranar Litinin.

A cewar babban jami'in na NITDA, na'uran da aka saka wa suna UnityBoard hanya ce ta inganta kowo da koyarwa da aka tsara saboda koyar da dalibai irin na zamanin yanzu saboda su samu kwarewa kan kirkire-kirkire da iya tunani.

DUBA WANNAN: Tsohon Farai Ministan Ingila ya fadi dalilin da yasa Jonathan ya hana a ceto 'yan matan Chibok

Ya ce, "Idan aka bawa dalibai dama suyi tunani da kansu su kirkiru sabbin abubuwa, za su fara ganin fasaha a matsayin hanya ta magance matsaloli na rayuwa."

Ya ce idan aka gabatar da fasahar sadarwar ta musamman a makarantu ta hanyar UnityBoard, zai sauya tsarin ilimin Najeriya baki daya.

Dagu ya ce, "Kasar ta mayar da hankali sosai kan fanin fasaha kuma cikin dan kankanin lokaci tattalin arzikin kasar zai inganta kamar yadda na kasashen da suka cigaba ya yi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel