Bidiyo: An kama wani dan siyasa da ranar Allah yana lalata da wata mata a otel

Bidiyo: An kama wani dan siyasa da ranar Allah yana lalata da wata mata a otel

- Wani bidiyo da yake ta faman a kafafen sadarwa na zamani ya bayyana yadda wani dan siyasa yake lalata da wata mata a otel

- Da bidiyon ya isa wajen dan siyasar ya bayyana cewa shi ba komai bane a wajen shi dan mutane sun ganshi a wannan yanayin

- Haka ita ma wata kakakin majalisa ta kasar Afrika ta Kudu ta bayyana cewa dukan su ba yara bane saboda haka ba komai bane dan sun aikata wannan abu

Wani bidiyo na wani dan siyasa dan kasar Afrika ta Kudu a lokacin da yake lalata da wata mata a otel ya yadu a kafafen sadarwa na zamano.

Jaridar Daily Sun, ita ce ta ruwaito, sai dai kuma ba ta bayyana ainahin sunan wajen da lamarin ya faru ba, amma ta bayyana sunan dan siyasar da Lawrence Seloane inda ita kuma matar aka bayyana sunanta da Tshepiso Maloka.

Da bidiyon ya isa wajen dan siyasar ya bayyana cewa shi bai damu ba dan mutane sun ga wannan bidiyon.

Haka ita kuma Maipato Tsokalibane, kakakin majalisar Emfuleni ta yi magana akan bidiyon, inda ta ce wannan bidiyo ba komai bane, ta ce dama ace su yarane da sai ayi Allah wadai da wannan abu da suka yi.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: An kama wata mata da taje za ta jefa 'ya'yanta guda biyu a cikin rijiya

"Dukansu baligai ne wadanda suka mallaki hankalin kansu, inda ace yara ne kanana dole zamu fito muyi magana akan wannan abu, ba mu san yadda aka yi bidiyon ba, an dauke su ne a lokacin da suke soyayyar su, kuma wanda ya dauka yana kokarin bata musu suna ne.

"Na san cewa duka suna da manyan matsayi, saboda haka zamu sanya kwamiti da za ta gabatar da bincike a kansu," in ji matar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel