Allah mai iko: Tayi nakuda har ta haihu a karkashin gada

Allah mai iko: Tayi nakuda har ta haihu a karkashin gada

- Abin mamaki da alhini ya auku a yankin Akobo na Ibadan, babban birnin jihar Oyo

- Mutane sun yi cincirindo suna kallon wata mata na nakuda a kasan gada

- Kamar yadda Olutoke Blessing ta sanarwa manema labarai, halin ko-in-kula da mijinta ya nuna mata ne ya jawo hakan

Abin mamaki da alhini ya auku a yankin Akobo na Ibadan, jihar Oyo a ranar Alhamis.

Mace mai shekaru 42 mai suna Olutoke Blessing ta haihu a motar tasi.

Kafin wani mutumin kirki ya sanya ta cikin tasin, mutane da yawa sun zagayeta suna kallon tsananin ciwon nakudar da take.

A yayin da Olutoke ta yi magana da Tribune Online a cibiyar kiwon da ke Alegongo, Akobo, ta ce wanda ya yi mata cikin ne ya nuna mata halin ko-in-kula.

KU KARANTA: Magidanci ya bankawa matarsa wuta

Olutoke ta ce, tun farkon cikin, mijinta ya nuna mata baya so inda ya shawarceta da ta zubar da cikin.

Matar ta ce, ta bar gidansu da ke Amuloko bayan da ambaliya tayi awon gaba da kayansu. Ita kadai ke dawainiya da yaronta mai shekaru 5 a duniya tare da mijinta tun 2013.

A kwancen da take a gadon asibiti, bata da inda zata nufa bayan an sallameta. Olutoke na neman tallafin 'yan Najeriya don samun kula da yaranta biyu.

"Ni na kula da yarona. Mijina tuni ya barni tare da yaron ya auri wata mata. Tun 2013 ya karbe kudin da nayi kokari na tara," ta kara da cewa.

"Ina zama da yar'uwata ne a yankin Rainbow amma ta ce in nemi wajen zama. Na je General gas, kasan gada ne lokacin da nakuda ta kamani. Ina bukatar taimako," In ji matar

"A watan Yuni, mijina ya yi min duka tare da bukatar in zubar da cikin. Na gama haihuwa. Ina bukatar taimako don kulawa da yarana. Na fuskanci kalubale da yawa." In ji Olutoke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel