Buhari ya yi kira ga ba yan Najeriya da kasashen waje kariya a Afrika ta Kudu

Buhari ya yi kira ga ba yan Najeriya da kasashen waje kariya a Afrika ta Kudu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, ya fara rangajin kai ziyara a Afrika ta Kudu, inda yayi kira ga a ba yan Najeriya da sauran yan kasashen ketare dake zaune kasar cikakken tsaro.

Buhari yayi Allah wadai da hare-haren da aka daukaka a Johannesburg, babban birnin Afurka ta kudu wanda yayi sanadiyar farfasa shagunan yan kasashen waje.

Ya nemi da a karfafa matakai don hana sake aukuwar makamancin haka anan gaba.

Buhari da takwaransa na kasar Afrika ta Kudu, Ramaphosa sun gana na tsawon lokaci don cimma manufar bunkasa dangantakar kasuwanci da kuma hadin kan a siyasance don bunkasa tattalin arzikin su.

KU KARANTA KUMA: Ban yi danasanin amsar kaye daga wajen Buhari ba - Jonathan

Za a kuma gudanar da wani taro tsakanin Buhari da yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu a babban dakin taro a ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoba, don sauraran bayanan kwararru da kuma bayyana kokarinsa na basu goyon baya.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai jagoranci wani zaman majalisar tattalin arziki na musamman a ranar Asabar.

Wannan rahoto na kunshe ne cikin sanarwar da wani babban jami'in gwamnati ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya na yunkurin kafa wani sabon tsari na dawo da kasafin kudin kasar daga tsakanin watan Mayu/Yuni zuwa Janairu/Dasumba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel