Yadda muka yi dambe da wani melamin bogi da yazo cire min Aljanu lokacin ina budurwa - Laila Ali Othman

Yadda muka yi dambe da wani melamin bogi da yazo cire min Aljanu lokacin ina budurwa - Laila Ali Othman

Shahararriyar matar nan da ta shahara wajen taimakon al'umma marayu da marasa karfi wato Laila Ali Uthman, kuma babbar kawa a wajen fitacciyar jarumar nan ta masana'antar Kannywood Hadiza Gabon, ta bayyana yadda ta sha fama da malaman gargajiya lokacin tana budurwa a yayin da ake yi mata kallon tana da aljanu bayan kuma abin ba haka yake ba.

Ga yadda Laila ta bayar da labarin yadda abin ya faru da ita:

"Ina so na baku wani labari ne, lokacin ina budurwa kowa na yi mini kallon ina da aljanu saboda lokacin ina da fada da ka tabo ni zamu yi rigima, amma kuma lokacin ina da tsoro sosai da mutum yayi kokarin duka na zan gudu.

"A lokacin sai aka kai ni wajen wani malamin gargajiya, ina jin kusan saboda haka ne yasa har yanzu ban yadda da irin malaman nan da suke cewa zasu cirewa mutum aljanu. Wannan ma abinda yasa na kasa mancewa da shine, saboda shi azzalumi ne, mai cin zarafin yara.

"Shi dai wannan malamin da nake zancen a jihar Bauchi yake, amma ba zan bayyana sunanshi ba saboda yanzu ina tunanin ya shiryu ya daina abinda yake.

"Shi malamin a lokacin yana tunanin idan ance kana da aljanu ba ka san abinda kake ba, akwai lokacin da aka kaini gidan shi watarana da dare, sai ya saka aka daure mini kafafuna guda biyu wasu mutane suka danne mini kafa, sai yake cewa Babana wai idan nayi tari ko na nuna abin yana damuna to akwai aljanu a jikina.

KU KARANTA: Tirkashi: Tun kafin kotu ta yanke hukunci Rarara ya fara yiwa 'yan Kwankwasiyya shagube

"Da ya saka mini na daure naga abin yafi karfina, sai na fara attishawa ina tari, sai ya bude bargon ya samu dorina ya dinga zabga mini, dana ji wuya ni kuwa na fara ihu na kama cinyar malamin nan na ciza, aikuwa ina cizon shi sai ya fadi shi da kishiyar Mamana da suka danne ni tare.

"Haka shi kuma wani malami da aka kaini wajen sa a can Maiduguri, shi kuma hada wasu jagwalgwalon sa yayi, yace wai idan na sha nayi amai to ina da aljanu, haka na danne zuciyata na ki yin amai din, sai nace wa Babana mu tafi babu abinda ke damuna, haka aka hado mana magunguna masu yawan gaske, ai kuwa muna dawowa gida na dinga amai na wannan abun dana sha.

"A karshe shawarar da zan bayar shine, ba kowane ake haifa daya ba, akwai yaran da ake haifa suna yin wasu abubuwa da ba kowane yake yi ba, hakan ba wai yana nufin suna da aljanu bane."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel