Adam Zango ya rantse da Al-Qur'ani don musanta zargin da wani malami ya yi masa

Adam Zango ya rantse da Al-Qur'ani don musanta zargin da wani malami ya yi masa

- Jarumin fina-finan Hausa, Adam Zango ya musanta zargin da wani malami ya yi masa

- Malamin ya zargi jarumin da lalata da yara mata 'yan kasa da shekaru 20 da zummar tantancewa don sanyasu a fim dinsa

- Zango ya rike Alkur'ani tare da rantsewa cewa malamin kazafi ya yi masa

Shahararren mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adam A. zango ya musanta zargin da wani malami ya yi masa na cewa yana neman mata 'yan kasa da shekaru 20 don tantancesu da zummar sanyasu a sabon fim dinsa.

Malamin ya ce jarumin ya fice masana'antar Kannywood ne saboda baya bukatar hukumomin tace fina-finai su tantance nasa.

Ya ce jarumin na lalata tarbiyar yara matan 'yan kasa da shekaru 20 ne.

A kwanakin baya jarumin ya bayyana ficewarsa daga masana'antar Kannywood ne saboda muzgunawa jarumai 'yan fim da mawaka da gwamnatin jihar ke yi.

KU KARANTA: Bill Gates ya bayyana abinda yafi bashi mamaki game da Dangote

A faifan bidiyon da Adam Zango ya saka a YouTube don maida martani ga malamin, ya rike Alkur'ani mai girma tare da zargar malamin da abinda bai sani ba.

"Na rantse da Allah, djk abinda ka (malamin) fada a kaina Karya ne. An tantance mutanen da za su shiga fim a masana'antar Kannywood fiye da sau 100 amma ban taba yi ba."

"Du k yarinyar da ka ga na saka a cikin fim dina ita ta kawo kanta ko kuma na ga wasu sun saka ta a fim ni ma na sanya ta. Idan kuma sabuwa ce ta kawo kanta, sai na tabbatar da izinin iyayenta kafin na saka ta."

Jarumin ya kalubalanci malamin da ya fiddo da shaidun cewa yana kai 'yan mata otal.

Jarumin ya kara da kiran manyan malamai irinsu Sheikh Ahmad Gumi, Sheikh Ibrahim Daurawa da Sheikh Abubakar Giro Argungun da cewa su ja kunnen malamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel