Babbar magana: Babu abinda na tsana a rayuwata fiye da namiji - In ji Huddah
- Wata budurwa 'yar kasuwa dake kasar Kenya ta bayyana yadda ta tsinci kanta a cikin tarkon maza
- Budurwar ta ce ta taso a rayuwarta babu wanda ta tsana a rayuwarta kamar namiji
- Ta ce lokacin da take karama a gabanta mijin mahaifiyarta yake cin zarafin mahaifiyarta kuma babu abinda ta iya
Huddah Monroe ta bayyana yadda a karshe ta fada tarkon maza duk da cewa ta taso da tsananin tsanar su a rayuwarta, bayan ta ga yadda mijin mahaifiyarta ya dinga cin zarafin mahaifiyarta a lokacin tana yarinya.
Budurwar 'yar kasar Kenya wacce take cikakkiyar 'yar kasuwa tace mutane basu bukatar wani abin koyi a rayuwarsu da zai taimaka musu su zama wasu, inda ta bayyana cewa ta taso a cikin mutane 'yan iska.
KU KARANTA: To fah: 'Yan Kudu sunyo caa akan Hausawa yayin da aka kama 'yan damfara guda 6 Hausawa a jihar Kano
Ta cigaba da cewa ta tuna lokacin da mutane suke nuna musu wariya saboda su talakawa ne basu da komai a wancan lokacin, ta ce sun kai matakin da mutane suna zuwa su basu kayan sakawa saboda basu da shi.
Ta ce: "Abinda nake so nace shine abinda ya faru da kai a baya ba yana nufin haka zaka cigaba da zama a rayuwa ba, idan ka bari ka cigaba da zama a yadda kake wannan laifinka ne, ka tashi ka fita ka zama wani, shi kuma Allah zai taimake ka."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng