Tirkashi: Ya kashe kansa akan ya fadi wasan Bet9ja

Tirkashi: Ya kashe kansa akan ya fadi wasan Bet9ja

- Wani mutum mai matsakaicin shekaru wanda aka fi sani da Papa Ebube ya kashe kansa akan wasan Bet9ja

- Makwaftansa sun ce ya rataye kansa ne sakamakon rashin nasarar samun makuden kudaden har naira miliyan 36

- Bet9ja dai wasa ne matasa suka saba yi, wasu kan yi nasara inda wasu kan yi asara

Wani mutum mai matsakaicin shekaru wanda aka fi sani da Papa Ebube mazaunin yankin Arita Lane a Yenagoa ya kashe kansa.

Mutumin, kamar yadda makaftansa suka sanar, ya kashe kansa ne ta hanyar rataya. Yayi hakan ne a sa'o'in farko na ranar Lahadi.

Kamar yadda mazauna yankin suka sanar, akwai yuwuwar ya kashe kansa ne saboda wasan Bet9ja. "Ya fadi wasan Bet9ja ne wanda akwai yuwuwar ya samar masa da naira miliyan 36."

Takardun da 'yan sanda suka samu bayan isarsu sun bayyana cewa mamacin ya kammala karatun jami'arsa, matukin keke napep ne kuma masoyin wasanni ne.

KU KARANTA: Tubabban 'yan ta'addan jihar Zamfara sun mika bindigogi 100 ga jami'an tsaro

Akwai sa ran Dan sa ya kammala karatu a makarantar sakandiren sojoji a wannan shekarar.

Papa Ebube ma'abocin barkwanci ne a yankin. Yana da mata biyu da yara biyu.

Wasan Bet9ja dai ba yanzu ya fara kawo ire-iren munanan labarai a cikin al'umma ba.

Matasa da dama sukan zuba makuden kudadensu da sa rana zasu samu ninkinsu. Duk da wasu masu sa'a kan yi nasarar samun makuden kudaden, wasu masu akasin nasarar kan tashi a tutar babu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel