Hadin kai: Zama tsintsiya madauri daya shi ne tushen cigaba - Osinbajo
- Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kansu
- Ya yi kiran ne a jawabinsa da ya gabatar yayin taron yaye daliban jami'ar jihar Osun
- Ya bayyana cewa mabudin cigaban nahiyar Afirka har yau a hannun Najeriya ta ke don haka dole ne mu hada kai duk da banbance-banbance
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce akwai matukar muhimmanci tare da amfani ga 'yan Najeriya idan kansu hade.
A jawabinsa na yayen daliban jami'ar jihar Osun a ranar Asabar 21 ga watan Satumba, Osinbajo ya hori 'yan Najeriya dasu cigaba da zama tsintsiya daya, madauri daya don ganin wanzuwar cigaba, kamfanin dillancin labarai ya ruwaito.
Ya yi nuni da rarrabewar kawuna a matsayin ci baya tare da cewa manyan kasashen duniya sun kai inda suke ne saboda hadin kai.
Ba gaskiya bane ace saboda dukkanmu munzo daga wurare daban-daban ya nakasa daidaituwarmu; bunkasarmu na daga yawanmu.
Gawurtattun kasashe sune wadanda kansu hade duk da banbance-banbancensu.
KU KARANTA: DPR ta rufe gidajen mai 12 a jihohin Sokoto da Kebbi
Ya ce: "Rabuwar kai ba zai zamo yadda zamu shawo kan matsalolinmu ba; hadin kanmu ne zai amfanemu. Najeriya na rike da Dan makullin cigaban nahiyar Afirka kuma har yau ita ke jagorantar yankin."
"Burinmu shi ne jagorantar Afirka da duniya. Don haka ne dole mu hada kawunanmu. Albarkatun Najeriya na fuskantar kalubale amma dole ne mu bi sahun da ya kai sauran manyan kasashen inda suke a yau."
Ya kara jaddada bukatar 'yan Najeriya su dubi cancanta ne ba yanki ba yayin zaben jagorori tare da saka hannayen jari a ababen kawo cigaba ga mutane.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng