Masu shara sun tsinci jariri sabon haihuwa a wajen zubar da shara

Masu shara sun tsinci jariri sabon haihuwa a wajen zubar da shara

Rahotanni sun kawo cewa wani jinjiri da aka jefar a wajen zubar da shara a Owerri, babban birnin jihar Imo ya mutu.

Jinjirin ya mutu ne a safiyar ranar Juma’a, 20 ga watan Satumba, a wajen zub da shara dake yankin Hardel Junction, wajen da aka yasar da shi.

An sami jini a jikin jinjirin wanda hakan ya nuna cewa a lokacin ne aka haife shi. An tsince jinjirin ne a cikin kwali ba tare da tufafi ba a jikinsa.

Majiya sun fada ma manema labarai cewa masu sharan titi ne suka tsince shi a mace.

Lamarin ya janyo cunkoso a mahadin hanyan yayinda masu moci da matafiya ke yunkurin kallon mataccen jinjirin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Atiku ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga yan Najeriya, ya sha alwashin samun nasara a kotun koli

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an gano yan sanda a wajen da lamarin ya afku.

Ba a sami kakakin rundunar yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu ba a waya domin jin karin bayani, amman wani babban jami’in dan sanda ya fada ma manema labara cewa yan sanda na kan gudanar da bincike kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel