Wani mutumi ya koka bayan tsallake rijiya da baya, yace wani fasto yayi masa biza na bogi

Wani mutumi ya koka bayan tsallake rijiya da baya, yace wani fasto yayi masa biza na bogi

Wani dan Najeriya da limamin coci ya damfara ya koka a shafin zumunta. Mutumin mai suna Emmanuel Aramide ya bayyana cewa faston ya gabatar masa da biza na bogi duk da cewar ya biya kudin biza na ainahi.

Mutumin ya je shafinsa na Facebook domin bayar da labarinsa. Yayi bayanin cewa ya shiga karkashin bincike daban-daban daga ofishin hukumar kula da shige da fice na Dubai na tsawon watanni uku sakamakon bizan bogi da aka yi masa.

Aramide ya bayyana cewa ya biya faston wanda ya kasance wakilin samar da biza makudan kudade domin ya samar masa biza mai inganci amma sai ya damfare shi sannan ya bashi na bogi.

Wani mutumi ya koka bayan tsallake rijiya da baya, yace wani malamin addini yayi masa biza na bogi
Wani mutumi ya koka bayan tsallake rijiya da baya, yace wani malamin addini yayi masa biza na bogi
Asali: Facebook

Ba tare da ya san aika-aikan da aka yi masa ba, Aramide ya kammala shirye-shiryen tafiyarsa sannan ya kare a hannun hukuma domin fuskantar bincike. Mutumin wanda ya shiga wani hari ya bayyana cewa ya fuskanci abubuwan da ba zai iya Magana akai ba saboda bizan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji da yan sanda sun mamaye ofishin Sahara Reporters a Lagas

A cewarsa, yan Najeriya da dama na tunanin abunda za su samu daga mutane ba tare da tunanin makomar abun ba. Yace wadannan rukuni na yan Najeriya ne ke bata wa sauran suna a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel