Tarihi zai kafu: Matashiya mai shekaru 26 ta shiga jerin sunayen kwamishinonin da za a tantance a majalisar jihar Kwara

Tarihi zai kafu: Matashiya mai shekaru 26 ta shiga jerin sunayen kwamishinonin da za a tantance a majalisar jihar Kwara

- Gwamna Abdulrahman Abdulrazak zai kafa tarihi

- Ya zabi matashiya mai shekaru 26 da kuma mata hudu a cikin jerin sunayen kwamishinoninsa

- Kolo za ta kammala hidimar kasarta nan da mako biyu inda zata fuskanci majalisar jihar don tantancewa

Gwamna Abdulrahman Abdulrazak na jihar Kwara ya mika sunayen mata 4 ga majalisar jihar a cikin jerin sunayen kwamishinoninsa.

Matan sun hada da Joana Nnazua Kolo mai shekaru 26 'yar karamar hukumar Edu ta jihar Kwara.

Kolo, mai shekaru mafi karanci a jerinsu, ta kammala digirinta na farko ne daga jami'ar jihar Kwara a shekarar 2018.

In dai majalisar ta tabbatar da ita, zata zamo mafi karancin shekaru a kwamishinonin Najeriya.

Kolo a halin yanzu tana hidimtawa kasarta a jihar Jigawa inda take koyarwa a makarantar kwana da ke Guri.

Majalisar jihar zata tantance ta ne bayan ta kammala hidimar kasarta nan da mako biyu.

KU KARANTA: Tirkashi: Soja ya hallaka dan sanda har lahira

Abdulrazak ya kara da zaben tsoguwar babbar manajar FBN Mortgage, Folashade Omoniyi, a matsayin sabuwar shugabar hukumar kudin shiga na jihar. Zata gaji farfesa Murtala Awodun, wanda wa'adin shugabancinsa ya kusa karewa.

Omoniyi tana da digiri har biyu daga jami'ar Obafemi Awolowo. Tana da gogewar shugabanci a fannin banki, talla, fasahar yada labarai da kasuwanci.

Omoniyi 'yar karamar hukumar Irepodun ce ta jihar Kwara.

Sauran matan da ke jerin sunayen kwamishinonin kwararru ne kuma jigo a siyasa. Sun hada da: Sa'adatu Modibbo-Kawu; Arinola Fatimoh Lawal; da Aisha Ahmad Pategi.

Modibbo-Kawu ta kammala digirinta na farko a shekarar 1997 daga jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto. Ta samu digiri na biyu akan kasuwanci daga jami'ar Ilorin tare da mallakar shaidu daga Penn Foster Career School Scranton da ke Amurka, Metropolitan Business and Management da ke Dubai.

Tana auren Ishaq Modibbo-Kawu, babban daraktan NBC kuma zata wakilci Ilorin ta kudu in majalisar ta tantance ta.

Arinola Fatimoh Lawal, ta kammala digirinta na farko daga folyteknic din jihar Kwara kuma ta jagoranci masan'antu da yawa da suka hada da Batool Nigeria Limited, Mohbalamira Nigeria Limited da MirMira Enterprise.

Aisha Ahman-Pategi kwararriya ce ta fannin kasuwanci. Tana da gogewar aiki na sama da shekaru 20.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel