Kwamitin JNPSNC ba ta cin ma yarjejeniya a kan kason sabon tsarin albashi ba

Kwamitin JNPSNC ba ta cin ma yarjejeniya a kan kason sabon tsarin albashi ba

Tattaunawar karin albashi da ake yi ta gamu da wani tasgaro bayan wasu ‘yan sauye-sauye da kwamitocin su ka yi a zaman da aka yi Ranar Litinin dinnan a babban birnin tarayya Abuja.

A karshen zaman da babban kwamitin hadakar nan na JNPSNC da ke kokarin shawo kan dabbaka karin albashin ya yi, mun ji bangaororin gwamnati da kwadago sun canza matsaya.

Gwamnatin tarayya ta amince ta karawa ma’aikatan da ke kan mataki na 7 zuwa 14 karin 11% bayan a baya an hakikance a kan karin kashi 9.5%. Winifred Oyo-ita ke jagorantar wannan zama.

Har ila yau gwamnati ta yi na’am da karin 6.5% daga 5.5% ga manyan ma’aikatan da ke kan mataki na 15, 16 da kuma 17. Wakilan ‘yan kwadago su ma sun fara sauka daga matsayar da su ke kai.

Mista Simon Anchaver wanda ke magana a madadin ma’aikatan kasar yace sun yarda a karawa ma’aikatan da ke kan mataki na 7 zuwa 14 karin 29% a maimakon kashi 30% da su ke hari a da.

KU KARANTA: Sanatan Kaduna ya caccaki tsare-tsaren noman Gwamnatin Najeriya

Anchaver ya ce a bangaren ma’aikatan da ke kan matakin karshe na 15 zuwa 17, sun hakura da karin 24% a madadin 25% da su ke bida a baya. Kawo yanzu dai ba a cin ma yarjejeniya ba.

Wakilin ‘yan kwadagon ya kuma bayyana cewa sun fadawa kungiyoyin TUC da NLC su shirya tafiya yajin aiki domin tsoron gwamnati ba za ta biya su bashin da su ke bi daga sabon karin ba.

Yanzu dai za a fadawa shugaban kasa yadda aka tashi inda kuma za a san matakin da za a dauka nan gaba. Kawo yanzu, an dauki dogon lokaci a na kokarin ganin yadda za a kara albashin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel