Abinda yasa aka samu jinkiri a kan batun sulhu da 'yan bindiga a Sokoto

Abinda yasa aka samu jinkiri a kan batun sulhu da 'yan bindiga a Sokoto

Kwamishinan harkokin tsaro na jihar Sokoto, Kwanel Garba Moyi (murabus) ya ce an jinkirta sulhun da gwamnatin ke yi da 'yan bindiga ne saboda tafiyarsu zuwa kasa mai tsarki domin aikin hajjin 2019.

Daily Trust ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan jihar da Kwanel Moyi ne suka jagoranci tawagar gwamnati wurin sulhun da 'yan bindigan kafin tafiyarsu Suadiyya.

Mataimakin gwamnan ne aka nada jagoran mahajjatan jihar inda shi kuma kwamishinan yana cikin tawagar gwamnatin da suka tafi kasa mai tsarki sauke farali na wannan shekaran.

A hirar da ya yi da manema labarai, ya ce 'yan bindigan sun kira shi a wayan tarho sau da yawa suna tambayarsa game da batun sulhun amma ya ce suyi hakuri ya dawo gida Najeriya kafin su cigaba.

DUBA WANNAN: Wata mace musulma bakar fata ta sake lashe zabe a Amurka

Ya ce, "Sun amince da sharrudan da muka basu kuma muma mun amince da nasu. Hakan yasa suka saki sama da mutum 20 da ke hannunsu ciki har da 'yan Najeriya da 'yan jihar Zamfara."

Sharrudan da suka bamu sun hada da gina musu Ruga, makarantu na yaransu da hanyoyin kiwon shanu da sauransu wadda duk kwamishinan ya amince da hakan kafin tafiyarsa.

Ya yi bayyanin cewa 'yan bindigan da ke kananan hukumomin Kebbe, Tureta da Dange-Shuni ba su cikin wadanda ake sulhun da su amma suma ana gayyatarsu don yin sulhun.

A cewarsa, wasu bata gari cikin Fulani ne suka kai harin baya-bayan nan a karamar hukumar Sabon Birni kuma 'Yan sa kai aka kai wa harin saboda har yanzu suna musgunawa Fulani duk da cewa anyi sulhu.

Ya bawa al'ummar jihar tabbacin cewa Gwamna Aminu Tambuwal zai yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu zaman lafiya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel