Ku daina rarrabar da kudin man fetur - NES ta fadawa gwamnatin tarayya

Ku daina rarrabar da kudin man fetur - NES ta fadawa gwamnatin tarayya

- Kungiyar tattalin arzikin Najeriya, NES, ta kalubalanci kasafin kudin man fetur na gwamnatin tarayya

- Kungiyar ta jinjinawa gwamnatin tarayya akan rufe iyakokin kasar nan da tayi

- Ta kara da cewa gano man fetur a kasar nan yakamata ya canza labarin cigaban Najeriya

Kungiyar tattalin arziki ta Najeriya, NES ta kalubalanci yanayin kason ribar man fetur da kwamitin kaso na asusun tarayya tayi.

Kungiyar tace hakan tozarta kadarorin Najeriya ne.

Kungiyar tace gano man fetur ba zai canza labarin cigaba na Najeriya ba.

Kungiyar ta bada shawarar ne a ranar Lahadi inda ta yi bayanin rufe iyakokin kasar nan da gwamnatin tarayya tayi wanda tace cigaba ne a Najeriya.

KU KARANTA: Kasar Afirka Ta Kudu za ta turo wakilai na musamman Najeriya

Shugaban kungiyar, Farfesa Tamuno Agiobenebo, ya sanar da matsayar kungiyar a Abuja yayin ganawa da manema labarai a taron kungiyar.

Agiobenebo yace, "Samuwar man fetur a Najeriya yakamata ace ta canza labarin cigaba na Najeriya. Amma kuma, ba mu fahimta daidai ba."

Shugaban kungiyar ya kara da kiran 'yan Najeriya da su zama masu kishin kasa tare da komawa sayan kayayyakin da aka samar da su a gida Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng