Samun nasara a kotu: Buhari bai yi 'mi'ara koma baya' a kan furucinsa ba - Fadar shugaban kasa

Samun nasara a kotu: Buhari bai yi 'mi'ara koma baya' a kan furucinsa ba - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta ce wasu jaridu da kafafen yada labarai sun wallafa wani rahoto marar tushe a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba, 2019, mai taken "Kotun sauraron korafin zabe: Buhari ya yi 'mi'ara koma baya', ya fadi gaskiya a kan yadda hankalinsa ya tashi kafin a yanke hukunci."

A cewar wani jawabi da mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya fitar, fadar shugaban kasa ta ce an tauye kalaman da shugaba Buhari ya yi a jawabin da ya gabatar yayin da ya karbi bakunci gwamnonin jam'iyyar APC da suka ziyarce shi domin taya shi murna ranar Juma'a.

Da yake kotun ta yanke hukunci ne ranar Laraba, ranar da shugaban kasa ya jagoranci zaman majalisar zartar wa ta tarayya (FEC), shugaba Buhari ya fada wa gwamnonin cewa: "na yi dace matuka saboda an yanke hukunci ne a daidai lokacin da nake gudanar da taron FEC na farko a zango na biyu na mulki na.

"Taron FEC na ranar ya kasance mai tsawo don ya dauki lokaci kamar yadda hukuncin kotun ya dauki lokaci kafin zartar da shi a ranar. Na gode wa Allah, saboda ba don haka ba da na shiga cikin yanayin zakuwa ko damuwa . Na tattara gaba daya hankalina na mayar da shi a kan takardun da ke gaba na yayin taron FEC."

DUBA WANNAN: Gara na taya Buhari murna a kan na kai masa ziyara, ba zan taba ziyartarsa ba - Wike

Adesina ya bayyana cewa, "duk wanda ke fahimtar harshen Turanci zai fuskanci cewa shugaba Buhari na magana ne a kan rana da lokacin da kotun ta yanke hukunci, ba kafin wannan rana ko lokaci ba."

Adesina ya koka a kan yadda jaridar 'Punch' da ke fito wa kowacce ranar Asabar da wasu sauran jaridu da kafafen yada labarai suka wuce 'makadi da rawa' wajen bayyana cewa shugaba Buhari ya yi amai ya lashe a kan furucinsa na farko da ke cewa ko kadan batun karar da Atiku da PDP suka shigar da shi a gaban kotu bai daga masa hankali ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel