Toh fah: An tambayi masu neman aikin dan sanda sunan Shugaban kasa da na Shugaban alkalai basu sani ba

Toh fah: An tambayi masu neman aikin dan sanda sunan Shugaban kasa da na Shugaban alkalai basu sani ba

Sola Okediji, mataimakin kwamishinan yan sandan Abuja, ya bayyana cewa wasu masu neman aikin yan sanda basu san sunayen shugaban kasar Najeriya da shugaban alkalan Najeriya ba.

Okediji ya bayyana hakan a taron horar da yan sandan Abuja, wanda kungiyar doka da yaki da rashawa RoLAC ta shirya a ranar Juma’a a Abuja.

Kungiyar tarayyar turai ce ke daukar nauyin shirin RoLAC .

Okediji, wanda yace an tura shi Rivers a Port Harcourt daga cikin wadanda za su yiwa masu neman aikin yan sandan jarrabawa domin su samu shiga Cikin rundunar, yace ya yi mamaki lokacin da ya ga wani mai neman aikin yan sandan ya gaza amsa tambayar da aka yi masa.

Ya bayyana cewa ya tambayi mai neman aikin “menene sunan shugaban kasar Najeriya”, amma ya gaza amsawa.

Okediji ya kuma bayyana cewa sake masa wata tambayar cewa “wanene shugaban alkalan Najeriya,” inda ya gaza ansawa.

Mataimakin kwamishinan yace bai da wani zabi da ya wuce korar shi anan take, inda ya kara da cewa rundunar yan sandan Najeriya ba za ta lamunci jahilci ba, inda ya kara da cewa irin wannan rashin sani ba abun yarda bane a hukumar yan sandan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawar sirri da gwamnonin APC

Okediji ya bayyana cewa wasu daga cikinsu na yawo da satifiket din jarrabawar SSCE wanda ba za su iya karewa ba.

Ya bayyana cewa ba za a bari wadanda basu san abubuwan da ke faruwa a kasar shiga rundunar yan sanda ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel