'Yan duba sun damfari wata mata naira miliyan 11

'Yan duba sun damfari wata mata naira miliyan 11

- Hukumar 'yan sandan birnin tarayya sun kama wasu 'yan duba 4 da laifin damfara

- Sun damfari wata mata har Naira miliyan 11 bayan sunce sun hango mata daukaka

- Matar ta sanar musu yadda basa zaman lafiya da mijinta don haka take da burin finsa kudi

A ranar Alhamis ne hukumar 'yan sandan birnin tarayya ta cafke 'yan duba hudu da laifin damfarar wata mata miliyan 11.

Kehinde Ayoola mai shekaru 37, Sesan Fatoye mai shekaru 30, Shola Samuko mai shekaru 50 da Seyi Fagbemi mai shekaru 32, sunce sun damfari matar ne bayan sun sanar da ita hango mata daukaka da suka yi.

Wacce aka damfarar ta bi masu damfarar ne har inda suke da burin haskawar rayuwarta nan gaba.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan birnin tarayyar, DCP Sunday Babaji yace: "Yan sanda sun kamo 'yan duban ne bayan da rahoton damfarar da suke yi ya isowa hukumar. A koken wacce suka damfarar, tace sun damfareta Naira miliyan 11 kafin ta sanar da 'yan sanda."

"Wajen aikin nasu na Waru, Pyakassa da kauyen Galadimawa. A yayin da hukumar ke kokarin kama sauran 'yan kungiyar, ana shawartar mutane da su kiyayi mutanen da kan taresu a hanya a matsayin 'yan duba."

KU KARANTA: Toh fah: Ta sace yaro daga gidan marayu tare da siyar da shi

Abubuwan da aka samu a wajensu sun hada da: Layu, magungunan gargajiya, kwarya, kyallaye farare da jajaye da kuma kwalabe.

A yayin da Kehinde Ayoola mai shekaru 37 daga jihar Ekiti ke bayyana yadda suka damfari matar: "Nazo Abuja a shekarar da ta gabata don siyarda magungunan gargajiya amma yanzu gani a ragar 'yan sanda akan damfara."

"Na sanar da ita na hango daukaka tare da ita kuma zan taimaketa wajen samunta. Ta yarda da zantuka na, don haka ina isa gida na ba oga na waya ya kara mata gamsassun bayanai. Ya umarceta da ta siyo bible da sauran abubuwa."

"Lokacin da tazo wajen aikinmu, mun sa ta rubuta abubuwa uku da take so. Tace tana son tayi kudi, ta daukaka kuma tayi suna. Tayi korafin cewa basa jituwa da mijinta don haka tana son tafi shi kudi."

"Da abubuwan da ta lissafo, sai muka fara aiki. Mun bukaci ta siyo akuya don ayi yanka. Bayan yankan sai muka ce muna bukatar giwaye 4."

"Ta bada Naira miliyan 1.6 tunda munce mata duk giwa daya N450,000 ake siyarwa. Bamu siyo giwa ba muka raba kudin tsakaninmu."

"Bayan nan ne muka bukaci naira miliyan 9. A satin da ya gabata ne ta kiramu akan karbar kudin. Daga zuwana 'yan sanda suka cafkeni."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel