Jami’o’in Najeriya 3 kacal ne suka yi nasarar shiga jerin manyan jami’o'i 1000 a duniya (kalli sunayensu)

Jami’o’in Najeriya 3 kacal ne suka yi nasarar shiga jerin manyan jami’o'i 1000 a duniya (kalli sunayensu)

- Makarantun Najeriya uku sun yi nasarar shiga jerin manyan jami’o’i 1000 a duniya

- Jami’ar Convenant ce kan gaba a jerin inda jami’ar Ibadan da jami’ar Lagas suka samu matsayi mabanbanta

- Anyi amfani kokarin makarantun ne a fannin koyarwa, bincike da sauran su

Wasu jami’o’in Najeriya uku sun shiga jerin manyan jami’o’i 1000 na duniya da.

Ma’aunin da aka yi amfani dashi wajen fitar da kididdigan sun kasance akan kokarin jami’o’in ta bangaren koyarwa, bincike, ilimi da kuma yadda suke samun karbuwa a duniya.

Daga cikin manyan jami’o’in Najeriya da suka samu shiga rukunin akwai jami’ar Convenant, wacce ita ce ta 401 a jerin.

Jami’ar Ibadan ce ta biyo baya a matsayin mafi kyawu a kasar inda take a tsakanin 501-600 sai kuma jami’ar Lagos wacce take a tsakanin 801-1000, kuma ita ce ta uku a kasar.

KU KARANTA KUMA: Jerin illoli 7 da ke tattare da shan ruwan sanyi ciki harda sa mutum tsufa da wuri

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya ceewa Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta zargi 'yan siyasa da gurgunta jami'o'in gwamnati a kasar ta hanyar shimfida tsare-tsare domin kare nartabar jami'o'in yan kasuwa da masu zaman kansu.

Zargin kungiyar na kunshe ne cikin wata sanarwa ta shugabanta, Farfesa Biodun Ogunyemi, lamarin da ya ce 'yan siyasa an ci gaba gurgunta jami'o'in gwamnati a kasar domin na 'yan kasuwa da na mazau zaman kansu su samu gindin zama.

Furucin Ogunyemi ya zo ne a yayin zantawa da manema labari bayan taron jiga-jigan kungiyar ASUU na kasa da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata cikin jami'ar tarayya ta nazarin noma da ke birnin Abeokuta a jihar Ogun.

Ya yi bayanin cewa, kungiyar yayin zaman majalisar zartarwa da ta gudanar, ta yanke shawarar watsi da sake kafa bankin ilimi na kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel