Karatun Al-Qur'ani yana kawar da damuwa da kuncin rayuwa - Ustaz Idris Ibrahim

Karatun Al-Qur'ani yana kawar da damuwa da kuncin rayuwa - Ustaz Idris Ibrahim

Wani shehin malamin addinin Islama a karamar Kirikasamma ta jihar Jigawa, Ustaz Ibrahim Idris, a ranar Asabar da ta gabata ya gargadi Musulmi da su ribaci karatun Al-Qur'ani a koda yaushe domin samun kariya ta kowane nau'in mugun nufi.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Ustaz Ibrahim ya bayyana hakan ne a garin Kirikasamma yayin kammala musabakar karatun Al-Qur'ani karo na 34 da aka gudanar a yankin.

A yayin da babu shakka Al-Qur'ani shi ne babban kundi mai warware dukkanin wasu matsaloli a doron kasa, shehin malamin ya ce karanta wannan littafi yana tsarkake zuciya da tunani, haka kuma yana kara hazaka da kaifin basira gami da inganta lafiyar jiki da saita tunani.

Haka kuma ya ce, karatun Al-Qur'ani bai takaita kadai ba wajen magance kunci da damuwa, kazalika yana magance cutar hawan jini, bugun zuciya, cutar zautuwa ko kuma gushewar hankali.

KARANTA KUMA: EFCC ta kama madamfaran yanar gizo 11 a jihar Delta

Ustaz Ibrahim wanda ya kasance babban alkali yayin musabar Al-Qur'ani da aka gudanar, ya gargadi dukkanin Musulmi a kan fa'idar haddace babban littafin da kuma fahimtar ma'anoninsa gami da aiki da dukkanin wata koyarwar da yayi tanadi.

Alhaji Bulama Kaku-Marma, sakataren ilimi a yankin Kirikasamma, ya nemi Iyaye da su sanya idanun lura a kan 'ya'yan su tare da tabbatar da sun dabi'antu da kyakkyawar tarbiyya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, wani haziki Umar Abubakar, shi ne ya lashe musabakar haddar Al-Qur'ani a rukunin Maza yayin da Rumasa'u Abubakar ta yi fintinkau a rukunin Mata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel