Shahararriyar mawakiyar gwambara, Nicki Minaj ta sanar da daina waka

Shahararriyar mawakiyar gwambara, Nicki Minaj ta sanar da daina waka

- Shahararriyar mawakiya Nicki Minaj ta yi Murabus daga waka

- Ta yi hakan ne bayan auren masoyinta Kenneth Petty

- Ba a waka kadai ta tsaya ba, shahararriyar mawakiyar ta fito a fina-finai daban-daban na Amurka

Shahararriyar mawakiyar gambara, Nicki Minaj ta ce "Na yanke hukuncin yin murabus don ajiye iyali".

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito cewa mawakiyar ta sanar da zancen yin murabus din ta a ranar Alhamis a shafinta na Twitter.

Ta ce, " Na yanke shawarar yin murabus don tara iyali. Na san kuna farinciki. Ga masoya na, ku cigaba yi na har bayan rai na."

"Ina son ku har abada," haka ta rubuta a shafin na ta.

Shahararriyar mawakiyar gambarar tana soyayya ne da Kenneth Petty kuma tuni suka nuna alamar suna shirin aure.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kai wa tawagar Gwamna Zulum hari

Bayan waka, mawakiyar mai shekaru 36 ta bayyana a fina-finai daban daban na Amurka.

Sai dai kuma bata bayyana cewa da gaske ta ke ba da abinda ta rubuta a shafin na ta.

A watan Augusta, yayin da ake shirin gidan rediyo da mawakiyar, tace ita da saurayinta zasu angwance nan da kwanaki 80.

Bayan sakin fayafayanta a cikin shekarun 2000, Nicki Minaj ta hade da Drake a ka kamfanin Lil Wayne na Young Money Entertainment.

Faifan wakokinta na 'Pink Friday' ya fito a shekara 2010. Bayan haka fayafayanta irinsu 'Super Bass' , 'Anaconda' da kuma 'Starships' wadanda ta fitar ita kadai a matsayinta na mashahuriyar mawakiyar gwambara a duniya.

Fayafayan wakokinta sun yi farin jini a kasuwa inda suka jawo mata miliyoyin kudi.

Ta yi wakokin hadin guiwa da Ludacris, Usher, David Guetta, Madonna Ariana Grande, Kanye West da Justin Bieber da sauran su.

Daga cikin fina-finan da ta bayyana a ciki sun hada da 'The Other Woman' da 'Ice Age: Continental Drift'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel