An kashe mutum 1 a sanadiyyar rikici tsakanin manoma da makiyaya a Jigawa

An kashe mutum 1 a sanadiyyar rikici tsakanin manoma da makiyaya a Jigawa

Akalla mutum daya ne ya mutu a sanadiyyar rikici daya kaure tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Iggi dake cikin karamar hukumar Birnin Kudu na jahar Jigawa, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansanda reshen jahar Jigawa, Bala Zama ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar dake garin Dutse a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 2 a wasu hare hare da suka kai a Borno

A cewar kwamishinan Bala, rikicin ya kaure ne a sanadiyyar sa’insa a kan wani katafaren fili wanda kowanne bangare ke ikirarin mallakinsu ne, kuma wannan fili yana yankin dajin Iggi ne.

Shugaban hadaddiyar kungiyar yan Fulanin Najeriya, Miyetti Allah Cattle Breeders Association reshen jahar Jigawa, Sa’idu Gagarawa ya tabbatar da aukuwar rikicin, sai dai ya bayyana lamarin a matsayin ramuwar gayya ga jibgar wasu Fulani 2 da manoma suka yi a kauyen Dangalma.

“Fulani makiyaya guda 2 sun ci dukan tsiya a kauyen Dangalma a hannun manoma, koda yan uwansu suka isa inda lamarin ya auku domin su cecesu sun tarar dasu ne kwance male male cikin jini, wannan ne ya tunzura matasan Fulani daukan fansa, inda suka kashe mutum 1.

“Shuwagabannin al’umma sun kashe rikicin daya dabaibaye mallakan wannan fili dake dajin Iggi, kuma sun mika ma Fulani ne, amma sai yanzu manoma suka sake tayar da maganan.” Inji shi.

Sai dai wani dan uwan wanda aka kashe ya bayyana cewa a duk lokacin da manoma suke kan hanyarsu ta zuwa gona sai Fulani makiyaya su kai musu farmaki, tare da kwace duk abin da suka gani a hannumu, idan kuma mutum ya ki su harbe shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel