Tsohuwa mai shekaru 74 za ta haifa tagwaye bayan shekaru 54 da aure

Tsohuwa mai shekaru 74 za ta haifa tagwaye bayan shekaru 54 da aure

- Tsohuwar mai shekaru 74 zata kafa tarihi a duniya

- Zata haifi tagwaye bayan shekaru 54 da aurensu amma babu haihuwa

- An yi wa tsohuwar dashe ne bayan da taga anyiwa mai shekaru 55 dashen kuma cikin ya tsaya

Tsohuwa mai shekaru 74 da aure za ta haifi tagwaye a yau Alhamis, a India bayan da tayi shekaru 54 da aure ba haihuwa.

Yerramatti Raja Rao zata haifi 'yan biyu a wani asibitin kudi da ke birnin Guntur a India. Tuni dai likitoci sun shirya tsaf don karbar haihuwar.

Haihuwar 'yan biyun zata shafe tarihin wata mata a 2015 mai shekaru 70 da ta haifa tagwaye.

Mace mafi tsufa a duniya da ta haihu 'yar kasar Italia ce mai shekaru 101 a duniya.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

Kamar yadda likitoci suka sanar, Yerramatti Raja Rao 'year Nelapartipadu a gabashin yankin Godavari ta auri Mangayamma ne a ranar 22 ga watan Maris, 1962.

Bayan shekaru kadan da aurensu, suka dinga tsammanin haihuwa amma shiru kake ji. Duk da tsufan da suka yi, burin samu 'ya'yansu bai cika ba.

Kwatsam sai ga makwafciyarsu mai shekaru 55 ta samu rabo bayan an dasa mata. Tuni tunanin Mangayamma ya koma kan haihuwa. Babu jimawa suka garzaya zuwa asibitin Ahalya dake birnin Guntur.

Bayan haduwarsu da kwararrun likitocin dasa kwayoyin halitta a mahaifa, sai aka dabi kwan maniyyin mijin aka gwada dasa wa matar. Tuni dai aka yi nasara inda cikin ya tashi har ya fara girma. Daga baya aka gano tagwaye ne a mahaifarta.

Bayan nan Dr. Umashankar ya yanke hukuncin yi mata aiki a yau alhamis da karfe goma da rabi don cire tagwayen.

"In dai Mangayamma ta haifi tagwaye, zata kafa sabon tarihi a duniya" cewar Dr. Umashankar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel