Shin Boko Haram za ta kai wa kasar Afirka ta Kudu hari na ramuwar gayya

Shin Boko Haram za ta kai wa kasar Afirka ta Kudu hari na ramuwar gayya

A wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta ruwaito, tun bayan fara kai wa baki farmaki da hare-hare na kin jini a farkon makon nan a Afirka ta Kudu, an ci gaba da samun wasu labarai na tatsuniya wadanda ke yaduwa a zaurukan sada zumunta musamman a Najeriya.

Ana ci gaba da yada tatsuniyoyi kan cewa kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, za ta kai wa Afirka ta Kudu hari a matsayin ramuwar gayya dangane da yadda wasu 'yan kasar suke kai wa baki munanan hare-hare na kin jinin su.

Sai dai a binciken manema labarai na jaridar BBC Hausa suka gudanar dangane da yaduwar wannan rade-radi, sun gano cewa babu ko alama ta kamshin gaskiya game da wannan ikirari na barazanar kai harin da Boko Haram za ta yi.

A cewar su, "iya bincikenmu babu wata sanarwa da ta fito daga kungiyar dangane da wannan labarin ta kafofin da suka saba fitar da sanarwa."

"Yanzu haka 'yan Najeriya da 'yan Afirka ta Kudu na sheke ayarsu a shafin Twitter da maudu'in #BokoHaramChallenge, inda suke yi wa juna tsiya game da labarin cewa Boko Haram za ta kai wa kasar hari."

"Da dama daga 'yan Afirka ta Kudun suna yin ba'a cewa su kam ba za su iya ja da Boko Haram ba saboda haka sun tattara kayansu sun fice daga kasar."

'"Yan Najeriya kuwa lissafa wasu wurare da abubuwa suke wadanda suke so Boko haram ta kai wa hari, ciki har da wannan matar mai cewa 'one minute remaining' - wacce take yin gargadi idan kudin waya sun rage saura minti daya."

Ana iya tuna cewa a ranar Larabar ta gabata ne shugaban kasa Buhari da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma ministan harkokin kasashen wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, suka shiga bayan labule dangane da tababar kin jinin baki da ake yi a kasar Afirka Ta Kudu, biyo bayan hare-haren da aka zartar kan 'yan Najeriya a kwana-kwanan nan.

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta aike wa jakadan Afirka Ta Kudu a kasar, Mista Bobby Moroe sammaci kan hare-haren kin jinin baki da ake kai wa 'yan Najeriya a kasar da yake wakilta.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ba za ta sake bari a taba kudin kananan hukumomi ba - Boss Mustapha

Haka zalika, ministan harkokin kasashen ketare, Mr Onyeama, ya gana da jakadan Afirka Ta Kudu a ranar Talatar da ta gabata kan kashe-kashe na baya-bayan nan da aka fara a karshen makon nan.

A cewar ministan, daga cikin matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka akwai batun hadin gwiwa a tsakanin jami'an tsaron kasashen biyu, lamarin da Ministan ya ce zai bai wa jami'an tsaron Najeriya da ke ofishin jakadanci Najeriya a kasar Afrika ta Kudu damar aiki tare da takwarorinsu na kasar domin bayar da kariya ga 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta kuma bukaci gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta fara biyan diyya ga dukkan 'yan Najeriya da hare-haren ya shafa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel