Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta kori karar dan takarar PDP, ta tabbatar da Bomai a matsayin sanatan Yobe ta Kudu

Yanzu Yanzu: Kotun zabe ta kori karar dan takarar PDP, ta tabbatar da Bomai a matsayin sanatan Yobe ta Kudu

Kotun sauraron kararrakin zabe na jihar Yobe, da ke zama a Abuja ta tabbatar da zaben Ibrahim Bomoi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin sanata mai wakiltan yankin Yobe ta kudu.

Kwamitin mutum uku na kotun zaben, ya yanke hukunci a ranar Laraba, 4 ga watan Satumba, cewa masu karar, Sanata Mohammed Hassan da jam’iyyarsa, Peoples Democratic Party (PDP) sun gaza tabbatar da ikirarinsu na cewa Bomoi bai lashe yawan kuri’un da ake bukata ba sannan cewa ba a gudanar da zaben daidai da dokar zabe ba.

Shugaban kotun zaben, Justis Susan Orji, wanda ya karanto hukuncin, ya yarda da lauyan Bomoi, Akinlolu Kehinde (SAN) cewa shaidar da shaidun masu kara suka bayar bai da fa’idar da kotun zaben za ta yi aiki dashi.

“A nazarin karshe, na riki cewa masu karar sun gaza tabbatar da shari’ansu. Don haka an kori karar,” Inji Justis Oji.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun saki shugaban matasan PDP da suka yi garkuwa dashi

A wani labari makamancin haka, mun ji cewa Kotun sauraron kararrakin zabe da ke zama a Makurdi, jihar Benue, ta jadadda nasarar Sanata Gabriel Suswam a zaben sanata mai wakiltan Benue ta arewa maso gabas.

Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Justis A. O. Odugu a ranar Talata, 3 ga watan Satumba, ya kori karar da dan takarar jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Mimi Orubibi, ya shigar inda yake kalubalantar zaben tsohon gwamnan a zaen ranar 23 ga watan Farairu, Channels TV ta ruwaito.

Kotun zaben ta kuma kori karar akan hujjar cewa mai karar yaki tabatar da zarginsa na magudi a tsarin gudanarwar zaben kaamar su magudin zabe da siyan kuri’u.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel