Tirkashi: Rikici ya barke yayin da matar wani dan siyasa ta kama mijinta dumu-dumu da karuwa a gado suna lalata

Tirkashi: Rikici ya barke yayin da matar wani dan siyasa ta kama mijinta dumu-dumu da karuwa a gado suna lalata

- Rikici ya barke yayin da wata mata ta kama mijinta dumu-dumu akan gado da wata karuwa suna lalata

- Matar ta dauki bidiyon yadda lamarin ya faru ta sanya a kafar sadarwa inda mutanen garin da take suka gani

- Mutumin dai an bayyana cewa dan siyasa ne a garin, inda dalilin wannan abu da yayi yasa aka cire shi daga kan mukamin da yake

Wani dan siyasa a kasar China na cire shi daga mukamin shi, bayan matarsa ta kama shi dumu-dumu akan gado da wata matar suna lalata. Bidiyon yadda lamarin ya faru ya yadu a kafar sadarwa a wannan satin.

Mutumin wanda yake babba ne a garin na Guizhou, an cire shi daga mukamin shi bayan manyan garin sun zauna sun yanke hukunci a tsakaninsu.

Mutumin mai suna, Jia Ding, an cire shi daga mukamin shi na sakataren jam'iyya na garin Yongle, wanda yake a yankin Xinpu dake birnin Zunyi.

KU KARANTA: Wata mata ta zagi Buhari da Osinbajo akan halin ko in kula da suka nuna wajen kashe 'yan Najeriya da ake a Afrika ta Kudu

Bidiyon yadda lamarin ya faru ya fara yawo a kafar sadarwa a ranar Larabar makon da ya gabata, bayan matar mutumin ta wallafa a shafinta.

Sai dai kuma 'yan uwan mutumin sun bayyana cewa wannan abu da ya faru kusan kowa yana yi, kawai na shi ne ya fito fili.

Yanzu haka dai ana cigaba da gabatar da bincike akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel