Babu wanda ke son dan Najeriya a duniya, ko a lahira ba za a yarda da mu ba - P-Square

Babu wanda ke son dan Najeriya a duniya, ko a lahira ba za a yarda da mu ba - P-Square

- Daya daga cikin fitattun mawakan P-Square ya wallafa wani rubutu a shafinsa na kafar sadarwa

- Mawakin ya wallafa rubutun ne bayan irin abinda yake faruwa a kasar Afrika ta Kudu na kisan 'yan Najeriya da ake yi

- Mawakin ya bayyana cewa yana ganin ko wutar jahannama ba za ta karbi dan Najeriya ba dalilin irin kiyayyar da ake nuna mishi

Paul Okoye daya daga cikin fitattun mawakan nan da suka yi tashe a shekarun da suka gabata wato P-Square, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na kafar sadarwa inda ya lissafo jerin kasashen da basu son 'yan Najeriya su zauna a cikinsu.

Hakan ya biyo bayan kisan da ake yiwa 'yan Najeriya da sauran baki na wasu kasashen a kasar Afrika ta Kudu.

Mawakin ya bayyana cewa yankin Amurka, Turai, Asiya, Afrika, kai hatta dan Najeriya ma baya so ya zauna da dan uwanshi dan Najeriya.

Mawakin a karshe ya ce shi yana tunanin ko wutar Jahannama ba za ta karbi 'yan Najeriya ba.

Wannan rubutu da mawakin ya wallafa ya jawo masa zagi a kafar sadarwa, inda wasu suka bayyana cewa hauka ne da rashin hankali irin na shi, bai kamata ace yayi irin wannan furuci ba.

KU KARANTA: Za a sayar da zirin gashin kan shugaban kasar Amurka na farko akan naira miliyan sha takwas (N18m)

A makon nan ne aka tashi mutanen kasar Afrika ta Kudu suna bin 'yan Najeriya suna kashewa suna kuma kone shagunansu, ko kuma su kwashe komai na cikin shagon su sanyawa shagon wuta.

Wannan daliline yasa wasu 'yan Najeriya dake nan gida Najeriya suka fara daukar fansar abinda ake yi, inda suke bin shaguna na kasar Afrika ta kudu suna yin barna aa ciki.

An bayyana cewa 'yan Najeriya na cikin wani hali a kasar Afrika ta Kudun, inda da yawa suna cikin daji a boye rai a hannun Allah, wasu kuma sun rasa inda za su sanya kansu saboda bala'in da suke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel