Kuma dai! Yan bindiga sun kai mumunan hari Takum, jihar Taraba, akalla mutane 12 sun halaka

Kuma dai! Yan bindiga sun kai mumunan hari Takum, jihar Taraba, akalla mutane 12 sun halaka

A yau Lahadi, akalla mutane 12 suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu yan bindiga suka kaiwa al'ummar kabilar Jukun dake karamar hukumar Takum na jihar Taraba.

Yan bindiga sun yi ayari zuwa wasu sassan Takum inda suka harbe mutane da dama, Daily Trust ta bada rahoto.

An samu labarin cwa yan bindigan sun shiga garin Takum ne daga jihar Benue. Wnai mazaunin Takum, Yakubu John, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun shiga da muggan makamai.

Ya ce sun hallaka sama da mutane 12 hakazalika an kashe da dama cikinsu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar DSP David MIsal ya tabbatar da rahoton inda yace jami'an Soji da yan sanda sun yi artabu da yan bindigan kuma sun hallaka da dama cikinsu.

Ya ce an kwantar da kuran yanzu kuma Takum na lafiya.

A bangare guda, Kimanin sa'o'i 24 bayan harin da yan bindiga suka kai jihar Taraba inda suka kashe mutane biyu, wasu yan barandan sun hallaka wani limanin Katolika, Rabaren David Tanko, a Kufai Amadu, karamar hukumar Takum ta jihar.

Limamin wanda yake hanyar tafiyarsa zuwa Takum domin zaman sulhu da wasu abokansa kan yadda za'a shawo kan rikicin da yaki ci yaki cinyewa tsakanin yan kabilar Jukun da Tibi, ya gamu da ajalinsa.

Tabbatar da hakan ga manema labarai, shugaban kwamitin, Shiban Tikari, ya bayyana cewa bayan sun kashehi, sai suka bankawa motarsa da gawarsa wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel