Hukumar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da diban ma'aikata, ta bayar da dalili

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da diban ma'aikata, ta bayar da dalili

- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da diban sabbin ma'aikata 1000 da ta fara

- Hukumar ta bayyana cewa ta yi haka ne don samun daman kawo karshen wani mataki a tsarin matakan diban aikin

- Hukumar ta sanar da cewa za ta kara kara bude shafin neman aikinta bayan da ta gama shirye-shiryen da ta ke yi

Hukumar 'yan sanda ta dakatar da diban ma'aikata 1000 da ta fara. A bayanin da mai magana da yawun hukumar. Ikechukwu Ani yayi, ya ce an yanke shawarar dakatar da diban ma'aikatan ne don ta kai karshen a tsarin matakin karshe na diban.

Ya ce hukumar za ta tsara yadda za ta diba ma'aikatan ne da kyau wanda hakan hakki ne da ya rataya a wuyansu. A don haka ne suka umarci masu ra'ayin aikin da su dakata.

DUBA WANNAN: Buhari ya bukaci a binciki kwangilar da ta jefa Najeriya a bashi har na $9.6bn

"Hukumar ta bukaci dakatawar mutane masu ra'ayin aikin har zuwa lokacin da hukumar za ta kara budewa," inji shi.

Ani ya ce "shawarar dakatarwar diban ma'aikatan don cike gurbin matsayi daban-daban a hukumar hakki ne da dokar kasa ta tabbatar a kan hukumar".

Idan zamu tuna, a shekarar 2017 ne tsohon sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ce hukumar 'yan sandan za ta diba ma'aikata 10,000 duk shekara don karfafa aiyukanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel