Ambaliyan ruwa: daki guda sukutum ya fada ma wata Matar aure a Jigawa

Ambaliyan ruwa: daki guda sukutum ya fada ma wata Matar aure a Jigawa

Wata matar aure mai shekaru 20 a Duniya, Malama Fatsuma Musa ta gamu da ajalinta a ranar Talata, 27 ga wayan Agusta sakamakon mamakon ruwan sama daya sauka, wanda ya yi sanadiyyar faduwar katangar dakinta a kanta.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a dakin mamaciyar dake kauyen Auno, cikin karamar hukumar Kafin Hausa na jahar Jigawa, a daidai lokacin da Fatsuma da mijinta, Musa Awaisu suke kwance suna barci.

KU KARANTA: Yan Najeriya na kashe naira biliyan 400 wajen biyan cin hanci da rashawa a shekara – ICPC

Ba tare da bata lokaci ba jama’a suka garzaya da ma’auratan zuwa babban asibitin garin Kafin Hausa, inda a can likitoci suka tabbatar da mutuwar Fatsuma, kamar yadda majiyar Legit.ng ta tabbatar.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ruwan sama aka sha kamar da bakin kwarya a daren, wanda hakan ya sabbab faduwar ganuwar dakin ma’auratan, amma yace koda suka garzaya dasu asibiti sun fita hayyacinsu.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar Jigawa, SP Abdul Jinjiri ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tuni Yansanda sun mika gawar Fatsuma ga yan uwanta domin su yi mata jana’iza, su binneta.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake samu a daminar bana, musamman a watan Agusta ya lalata dubun dubatan gonakan manoma a jahar Jigawa, musamman a karamar hukumar Malammadori.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a wasu kauyuka guda 9 dake karamar hukumar Malammadori, inda ruwan ya lalata akalla eka 12, 000 na gonakan jama’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel