Gwamnatin jihar Kano zata samar da gidaje guda 2,000 masu saukin kudi domin talakawan jihar

Gwamnatin jihar Kano zata samar da gidaje guda 2,000 masu saukin kudi domin talakawan jihar

- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudurinta na samar da gidaje guda dubu biyu a fadin jihar domin samawa talakawa saukin rayuwa

- Gwamnatin ta bayyana hakan ne a kokarin da take na ganin ta mayar da jihar Kano tamkar birnin Abuja

- Wadannan gidaje dai tuni aikinsu yayi nisa, inda ake aikin a Kwanar Gurjiya dake karamar hukumar Dawakin Kudu

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ta bayyana kudurinta na samar da gidaje guda dubu biyu a fadin jihar.

A kokarin da gwamnan jihar yake yi na ganin ya bunkasa jihar ta Kano, inda yake so ta zama tamkar birnin Abuja, gwamnatin jihar ta ce za ta samar da gidaje masu rangwamen saukin kudi domin al'ummar jihar Kano.

Wannan gidaje za a bayar da su ga al'ummar jihar ne musamman ma'aikata da masu kananan karfi dake jihar domin more wannan rahusa ta gidajen.

KU KARANTA: Zan iya kare rayuwata ba tare da da namiji ya kusance ni ba - Najwat

Wannan gidaje dai an kerasu ne a yankin Kwanar Gurjiya dake karamar hukumar Dawakin Kudu, yanzu haka dai aiki yayi nisa na samar da wadannan gidaje.

Wannan sanarwa dai ta fito daga bakin shugabar mata a bangaren yada labarai ta jihar Kano, Safeeya Idris Darki, wacce ta wallafa hakan a shafinta na Facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel