Zan iya kare rayuwata ba tare da da namiji ya kusance ni ba - Najwat

Zan iya kare rayuwata ba tare da da namiji ya kusance ni ba - Najwat

- Wata budurwa ta bayyana cewa za ta iya rayuwa ba tare da ta kusanci naamiji ba har ta mutu

- Budurwar mai suna Najwat ta bayyana hakane a shafinta na Facebook

- Wannan magana ta budurwar ta kawo kace-nace matuka a shafukan sadarwa

Wata budurwa mai suna Najwat ta bayyana cewa za ta iya rayuwa ba tare da da namiji ya kusance ta ba.

Najwat ta bayyana hakan a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na kafar sadarwa na Facebook, inda ta ce "Bai zama dole sai da namiji zan rayu ba, domin kuwa ina ji a raina zan iya rayuwa ba tare da da namiji ba."

Wannan rubutu da budurwar ta wallafa ya kawo kace nace matuka a shafukan sada zumunta, inda mutane suka dinga mayar mata da martani kala-kala akan wannan rubutu da ta wallafa.

Wata mace mai suna Maryam Abdu Ali tayi sharshi akan maganar budurwar ta ce: "Dole mace ta yarda za ta rayu da namiji haka shima namiji mutukar ana so aga daidai, tunda Allah ne ya tsara hakan, saboda haka na kalubalance ki 'yar uwa matukar kina da lafiya."

KU KARANTA: Sun yaudare ni na tafi Turai sun kuma tilasta ni nayi karuwanci - Inji wata budurwa

Shi kuma wani namiji mai suna Ashraf Abdullahi cewa yayi: "Cikin abubuwa uku watakila tana fama da daya, na daya ko tana da iskokai, na biyu ko bata da lafiya, na uku ko kuma tana mu'amala da mata 'yan uwanta ne."

Shima Aminu Turaki cewa yayi: "Ina jin ke 'yar madigo ce, amma ki sani maza rahama ne a gareku haka muma ku rahama ne a garemu dole in dai ke cikakkiyar Musulma ce to ki yadda da cewa dole kiyi aure har kiyi rayuwa da da namiji kuma ki haifi da namiji."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: