Ruwan sama ya hana samuwar wutar lantarki a Kano - KEDCO

Ruwan sama ya hana samuwar wutar lantarki a Kano - KEDCO

Daga karshen makon da ya gabata kawo wa yanzu, ana ci gaba da karancin samun wadatacciyar wutar lantarki a birnin Kano da kewaye, lamarin da ya sanya da kamfanin rarraba wuta na jihar KEDCO, yayi karin haske na fayyace dalilin wannan cikas da al'ummar jihar ke fuskanta.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano KEDCO, ya alakanta saukar ruwan sama na mamako da rashin samun wutar lanarki a yankunan jihar da a baya suka saba da wadatacciyar wutar lantarki.

A sanarwar da kakakin KEDCO, Ibrahim Shawai ya gabatar, ya ce kamfanin ba zai gushe ba wajen ci gaba da jajircewa domin biyan bukata ta gamsar da abokanan huldarsu da kuma bunkasa tattalin arziki a jihohin Kano, Jigawa da kuma Katsina.

Sai dai kamfanin cikin bayyana rashin dadi, ya alakanta matsanancin rashin wutar lantarki da ya mamaye wasu yankuna a manyan biranen uku da nakasun samuwar wuta daga kamfanonin masu samar da wutar lantarki.

Shawai ya ce an yi rashin dace na rashin samuwar wutar lantarki yayin da ta fadi kasa daga nauyin mega watts 3,578 zuwa nauyin mega watt 3,014.8 a watan da muke ciki na Agusta.

KARANTA KUMA: Masu hada-hadar yanar gizo sun koka da sabon tsarin harajin Buhari

Hakazalika, ya alakanta hauragiyar kudi da ta kunno kai a tsakanin kamfanin rarraba wutar lantarkin na KEDCO da kuma kamfanin samar da wutar lantarki na kasa baki daya, TCN (Transmission Company of Nigeria).

A halin yanzu hauragiyar ta yi kamarin gaske yayin da kamfanin TCN ya sauke wasu injina biyu na rarraba wutar lantarki mallakin KEDCO kamar yadda Shawai ya bayyana.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel