Abin Al'ajab, an gano gawar da bata rube ba bayan shekaru 22 da rasuwa

Abin Al'ajab, an gano gawar da bata rube ba bayan shekaru 22 da rasuwa

- Abin al'ajabi! An samu wata gawa garas bayan binneta da shekaru 22

- Mutanen yankin sun kwatanta hakan da mu'ujiza

- Anyiwa mamacin shaidar zama mutumin arziki a lokacin rayuwarshi

A yankin Baberu na Banda ne aka samu gawa da ta shekara 22 a kabari garas! Gawar Nasir Ahmed, na nan bata yi komai ba, hatta likkafanin fari yake tas.

'Yan yankin na kiran wannan lamari da "karaama" kuma suna cewa a lokacin rayuwar mamacin ya kasance mutumin kirki.

Lamarin ya auku ne a ranar laraba a makabartar Baberu inda kabarin ya zurma bayan mamakon ruwan sama.

An sanar da kungiyar masu kula da makabartar, inda suka garzayo don yin gyare-gyare. A nan ne fa suka gamu da abin al'ajabin, inda suka ga gawa cikin farin likkafani.

KU KARANTA: 'Yansanda sun gano manyan bama-bamai tun yakin basasa

Nan da nan kuwa jama'a suka taru a wajen inda aka fito da gawar Nasir Ahmad, wanda ya rasu shekaru 22 da suka gabata.

Daya daga cikin 'yan uwan mamacin ne ya gane gawar kuma ya tabbatar da ya halarci jana'izar.

Bayan tuntubar malaman addini, daga baya aka kara binne gawarshi a daren ranar laraba.

Dama dai, dukkan mamacin da aka ga gawarsa bata baci ba, ana sa masa rai da lallai mutumin kirki ne, kuma yanacikin rahamar ubangiji.

Manyan salihan bayi da dama, a zamunnan baya, an sami gawarwakinsu cikin aminci, inda kuma shakiyyai akan ga macizai da kunami a ramukansu tun ma ba'a kjefa su ba, Allah shi tsare mu da muguwar rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel