Karya ne, ban fadi hakan ba - Sheikh Fantami ya karyata rahoton cewa zai fitar mutane milyan 50 daga talauci

Karya ne, ban fadi hakan ba - Sheikh Fantami ya karyata rahoton cewa zai fitar mutane milyan 50 daga talauci

Sabon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ibrahim Ali Fantami ya karyayta rahoton da wata jarida ta wallafa kansa cewa ya lashi takobin fitar da yan Najeriya milyan 50 daga cikin talauci a Najeriya.

Shahrarren malamin addinin kuma kwararren farfesan sadarwan ya karytata wannan labari ne da safiyar Asabar, 24 ga watan Agusta a shafinsa na Tuwita. Ya ce gaba daya bai yi magana a kan hakan ba, innama sakataren ma'aikatar ne yayi ishara akan hakan.

Ya ce ma'aikatar zata gabatarwa Najeriya takardan ayyukan da za ta gudanar domin su karanta kuma su fahimci inda suka dosa.

Yace: "Labarin da jaridar The Nation ta wallafa ba gaskiya bane kuma yaudara ne. Ban fadi hakan ba, saboda haka ayi watsi da shi. Abinda nike yanzu shine fahimtar ma'aikatar.

Baya ga haka, zamu gabatarwa yan Najeriya abubuwan da mukayi nufin yi domin su karanta. Sakataren din-din-din ne yayi magana akan al'amarin a matsayin shawara."

KU KARANTA: Buhari zai shilla kasar Japan, zai halarci taron TICAD7

Mun kawo rahoton cewa Ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami ya shiga sabuwar ofishinsa domin fara aiki.

Ministan yayi kira ga ma’aikatansa da cewa su zage dantse domin samu damar cika aiki da Shugaba Muhammadu Buhari ya daura a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel