Buhari ya saka hannu a kan kudirin kashe biliyan N600 don inganta lantarki a Najeriya

Buhari ya saka hannu a kan kudirin kashe biliyan N600 don inganta lantarki a Najeriya

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sakar wa bangaren hasken wutar lantarki tallafin biliyan N600

- Wannan shine karo na uku da gwamnatin tarayya ta bayar da tallafi mai tsoka ga bangaren wutar lantarki tun bayan sayar da shi ga 'yan kasuwa a shekarar 2013

- Majalisar dattijai ta sha nuna adawar ta da bayar da tallafin makudan kudi ga bangaren wutar lantarki bayan sayar da shi ga 'yan kasuwa masu zaman kansu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya saka hannu a kan kudirin amince wa da sakin zunzurutun kudi da yawansu ya kai biliyan N600 domin inganta samar da wutar lantarki a Najeriya.

Kamfani da ke raba wutar lantarki ga kamfanonin da aka sayar wa wutar lantarki (Transmission Company Of Nigeria (TCN)) ne ya sanar da hakan yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a bangaren wutar lantarki.

DUBA WANNAN: Asiya da Atika, kwararrun masu garkuwa da mutane sun shiga hannu a jihar Kebbi

Wannan shine karo na uku da gwamnatin ta bayar da tallafi ga bangaren harkar wutar lantarki tun bayan sayar da bangaren ga 'yan kasuwa masu zaman kansu a watan Nuwamba na shekarar 2013.

Sai dai, majalisar ta sha nuna adawar ta a kan bayar da tallafin kudi ga bangaren wutar lantarki da gwamnatin tarayya ke yi bayan ta sayar da bangaren ga 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel