Yanzu-yanzu: An fara rantsar da ministoci, an rantsar da sakataren gwamnatin tarayya

Yanzu-yanzu: An fara rantsar da ministoci, an rantsar da sakataren gwamnatin tarayya

An rantsar da Abubakar Malami, Ramatu Tijjani, Alhaji Lai Mohammed, Gbemisola Saraki, Adeleke Mamora, Babatunde Fashola, Abdullahi Mohammad Hassan, Zubairu Dada, Tayo Alasoadura, Rauf Aregbesola, Sunday Akin Dare, Paullen Tallen, Rotimi Amaechi.

An rantsar Mahmoud Mohammed, Zainab Ahmad Shamsuna, Sabo Nanono, Bashir Salihi da Hadi Sirika.

An rantsar da Malam Adamu Adamu, Ambasada Maryam Katagum daga Bauchi, Temipre Sylva, Mustapha Baba Shehuri, da George Akume.

An rantsar Otunba Adebayo, Geoffrey Onyeama, Sheik Isa Pantami, Chkwuemaka Nwajuba, Engr Suleiman Adamu.

An rantsar da Godwin Agba, Festus Keyamo, Ogbonnaya Onu, Osagie Ehanire, Clement Agba Ikanade.

An rantsar da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Cigaba: An rantsar da Uche Ogar, Chris Ngige, Godswill Akpabio, Muhammadu Musa Bello da Sharon Ikeazor.

Sabbin ministoci sun isa fadar shugaban kasa Aso Villa birnin tarayya Abuja misalin karfe 10:25 na safe cikin manyan motoci biyu daga Transcorp Hotel.

An tara su da iyalansu a Transcorp Hotel domin wani karamin tantancewa. Ana saukesu suka shige dakin taron da za'a rantsar da su.

Majalisar dattawan Najeriya ta tantance ministoci 43 da Buhari ya aika musu ranar 30 ga Yuli, 2019.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; jigon APC Ahmad Tinubu sun isa farfajiyar taron.

Ministocin sune:

Abia - Chkuwuwka Ogar : Karamin ministan ma'adinai

Adamawa - Muhammad Bello : Ministan birnin tarayya Abuja

Akwa Ibom - Godswill Akbapio - Ministan Neja Delta

Anambara - Chris Ngige - Ministan Kwadago da daukan aiki

Anambra - Sharon Ikeazu - Karamar ministar Yanayi

Bauchi - Adamu Adamu - Ministan Ilimi

Bauchi - Maryam Katagum - Karamar ministar Hannun Jari, masana'antu da kasuwanci

Bayelsa- Temipre Sylva - Karamin ministan man fetur

Benue - George Akume - Ministan ayyuka na musamman

Borno - Mustapha Shehuri - Karamin minstan noma

Cross Ribas - Agba - Ministan wutan lantarki

Delta - Festus Keyamo SAN - Karamin ministan Neja Delta

Ebonyi - Dr Ogbnayya Onu - Ministan Kimiya da fasaha

Edo - Osagie Ehanire - Ministan Lafiya

Edo - Clement IK - Karamin ministan kasafin kudi

Ondo - Otunba Richard Adeniyi - Ministan Hannun Jari, masana'antu da kasuwanci

Enugu - Geofreey Onyeama - MInistan harkokin wajen Najeriya

Gombe - Isah Ali Pantami - Ministan sadarwa

Imo - Emeke Nwajuba - Karamin ministan Ilimi

Jigawa - Suleiman Adamu - Ministan Ruwa

Kaduna - Zainab Shamsuna - Ministar Kudi

Kaduna - Muhammad Mahmud - Ministan Yanayi

Kano - Sabo Nanono - Ministan Noma

Kano- Bashir Salihi - Ministan Tsaro

Katsina - Hadi Sirika - Ministan Sufurin Jirage sama

Kebbi- Abubakar Malami - Ministan Shari'a

Kogi- RamatuTijjani - Karamar ministar Abuja

Kwara- Lai Mohammad - Ministan labarai da al'adu

Kwara- Gbemisola Saraki - Karamar ministar Sufuri

Lagos- Babtunde Fashola - Ministan aiki da gidaje

Lagos- Olorunnibe Mamora - Karamin ministan lafiya

Niger- Ali Dada - Karamin ministan harkokin wajen Najeriya

Nasarawa - Mohammad Abdullahi - Karamin ministan Kimiya da fasaha

Ogun- Lekan adebiti - Ministan ma'adinai

Ondo- Alasodura Tayo - Karamin ministan kwadago

Osun- Rauf Aregbesola - Ministan harkokin cikin gida

Oyo- Sunday Dare - Ministan matasa da wasanni

Plateau- Paulen Tallen - Ministar harkokin mata

Rivers- Rotimi Amaechi - MInistan Sufuri

Sokoto - Maigari Dingyadi - Ministan harkokin yan sanda

Taraba - Saleh Mamman - Ministan wutan lantarki

Yobe - Abubakar A ALiyu - Karamin ministan ayyuka

Zamafara - Sadiya Umar Faruk - Ministar tallafi da annoba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel