Khul’i: Kotu ta umurci wata matar aure da ta dawo da kafet da katifar da ta karba daga mijinta a matsayin sadaki

Khul’i: Kotu ta umurci wata matar aure da ta dawo da kafet da katifar da ta karba daga mijinta a matsayin sadaki

Wata kotun shari’a da ke Kaduna a ranar Talata, 20 ga watan Agusta ta umurci wata matar aure, Hauwa’u Zailani, akan ta dawo da kafet da katifar da ta karba a matsayin sadakinta daga tsohon mijinta, Akilu Yakubu.

Alkalin kotun, Malam Muhammad Shehu-Adamu, ya bayar da umurnin ne bayan Zailani ta fada ma kotu cewa bata muradin ci gaba da zama da mijin nata saboda rashin kula.

“Don haka soke auren da ke tsakanin Hauwa’u Zailani da Akilu Yakubu bisa Khul’i. Za ta dawo masa da sadakinsa,” inji hukuncin.

Zailani wacce ke da zama a kauyen Gandarko, jihar Kaduna, ta fada ma kotun cewa Yakubu ya yasar da ita lokacin da take rashin lafiya da laulayin ciki.

Ta bayyana cewa ta shafe watanni takwas a gidan iyayenta ba tare da jin doriyar mijin nata ba har sai da tayi bari.

Ta roki kotu akan ta kashe auren. A nashi bangaren, Yakubu, wanda ke zama a kauyen Kabobo, Kaduna, ya karyata ikirarin, cewa matarsa ta fada mashi cewa za ta je gida neman magani ne.

Ya roki kotu da ta bashi lokaci domin ya sasanta da matarsa, cewa har yanzu yana kaunar ta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe mutane 6 a Jigawa

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kotun ta bukaci masu korafin akan su gabatar da shaidu bayan duk wani kokari na sasanta ma’auratan ya ci tura.

Shaidan da ta gabatar ya tabbatar da cewa mijin ya yasar da Zailani a lokacin da take rashin lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel