Wasu yan gargajiya sun fitittiki limami da mamu daga masallaci

Wasu yan gargajiya sun fitittiki limami da mamu daga masallaci

Wasu masu bautan gunki sun kai hari masallacin khamsu salawati dake Ido-Iroko, karamar hukumar Ipokia na jihar Ogun inda suka yiwa limami da mamu jifan shaidan.

Jaridar Punch ta tattara cewa yan gargajiyan sun fitittikin mabiya addinin Islaman ne saboda sun fito Sallah lokacin da suke gudanar da wani bikin bautar gunkinsu duk da cewa sunyi gargadi kada kowa ya fito.

Shugaban al'ummar Musulmi na kasar Yarbawa, Edo da Delta, Sheik Iskeel Lawal, ya bayyana cewa wannan abu ya faru ne yayinda yan'uwa Musulmai suka fito sallatan Sallar Azahar a masallacin.

Ya ce dalilin da sa hakan ya faru shine yan gargajiya sun gargadi jama'ar unguwar cewa kada wanda ya fito ranar Asabar da zasu gudanar bikin bautar gunkinsu. Da farko Musulman basu fito ba amma daga baya sai suka fito Sallar Azahar.

KU KARANTA: Tabbatar da tsaro: Abubuwa 9 da ya kamata a kiyaye yayin tukin mota cikin ruwan sama - FRSC

Sheik Lawal yace: "Wannan abu ya faru misalin karfe 1:18 na rana ranar Asabar inda yan'uwa Musulmai suke Sallar Azahar a masallacin Umar bin Khattab a Odan-Aje, bayan asibitin Idi-Iroko."

"Masu bautan gunkin Oro sun kai farmaki masallacin ne inda suka yiwa limami da mamu jifan shaidan , suka korasu daga masallacin. Sannan suka barnata kayayyakin masallaci."

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da wannan labari kuma ya ce hukumar ta damke wasu daga cikin yan gargajiyan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel