Majalisar dattawa za ta sayo motocin naira biliyan 5.5 don amfanin Sanatoci

Majalisar dattawa za ta sayo motocin naira biliyan 5.5 don amfanin Sanatoci

Majalisar dokokin Najeriya ta kammala shirye shiryen sayo motocin alfarma da kudinsu ya kai naira biliyan 5.5 domin amfanin Sanatocin majalisar dattawa, inji rahoton jaridar Guardian.

Wata majiya daga majalisar ta bayyana ma majiyar Legit.ng cewa shuwagabannin majalisar sin fara tattaunawa a kan lamarin ne tun kafin Sanatocin su tafi hutun makonni 8 da suka fara bayan tantance ministocin Buhari.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta sauya sunan hukumar kula da gidajen yarin Najeriya

Sai dai majiyar ya kara da cewa majalisar za ta zare kudin motocin daga kudaden alawus din Sanatocin ne, a hankali a hankali, ya cigaba da cewa motar da aka fi gamsuwa a sayo ma Sanatocin ita ce Toyota Land Cruiser kirar Jeep, wanda kudinta ya kai naira miliyan 50.

Bayanai sun tabbatar da cewa majalisar za ta saya ma shuwagabannin kwamitocinta da mataimakansu motocin ne kawai, amma duba da cewa a yanzu haka kwamitocin majalisar sun kai 69, hakan na nufin kowanni Sanata daga cikin Sanatoci 109 zai samu wannan mota kenan.

An taba sayo ma Sanatocin majalisa ta 8 irin wadannan motoci a zamanin shugabancin Sanata Bukola Saraki, inda majalisar ta kashe naira biliyan 4 wajen sayosu, sa’annan bayan kammala wa’adin majalisar ta sayar da motocin a kan kudi naira miliyan 1 ga kowanne Sanata, alhali an sayosu ne a kan naira miliyan 36 kowanne.

Amma duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin majalisar dattawa, Sanata Adedayo Adeyey ya ci tura, sakamakon baya daukan wayarsa, kuma bai amsa sakon kar ta kwana da ta aika masa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel