Ko nawa ne: Kungiyar yan Shi’an kasar Indiya sun yi alkawarin biyan kudin asibitin Zakzaky

Ko nawa ne: Kungiyar yan Shi’an kasar Indiya sun yi alkawarin biyan kudin asibitin Zakzaky

Wata kungiyar yan Shia dake kasar Indiya, Anjuman-e-Haideri sun dauki alwashin daukan nauyin kudin asibitin Zakzaky da matarsa Zeenatu, da kulawa dasu yayin zaman jinyar da za su yi a asibitin kasar Indiya.

A ranar Talata, 13 ga watan Agusta ne Zakzaky da matarsa Zeenatu suka isa wani babban asibitin kasar Indiya dake birnin New Delhi, Medanta Hospital domin samun kyakkyawan kulawar data dace sakamakon rashin lafiya da suke fama dashi.

KU KARANTA: Tambuwal ya raba ‘Goron Sallah’ naira miliyan 70 ga alhazai 3,496

Wata babbar kotun jahar Kaduna ce ta baiwa Zakzaky da matarsa daman su tafi kasar Indiya domin samun kulawar data dace biyo bayan korafin da lauyoyinsu suka yi, inda suka ce mutanen biyu na fama da matsanancin rashin lafiya, kuma basu samun kulawa a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar yan Shi’an Anjuman-e-Haideri, Bahadur Naqvi, ya fitar, ya bayyana cewa ya aika ma shugaban asibitin Medanta, Dakta Naresh Trehan, wasikar neman daman biya dukkanin kudaden da ake bukata wajen kulawa da Zakzaky da matarsa a asibitin.

“Maulana Ibrahim Al –Zakzaky, wanda ya kasance jagora ne a Shia duba da dubun dubatan mabiya da yake dasu a duniya gaba daya, yana asibitinku don duba lafiyarsa, don haka majalisar zartarwa ta Anjuman-e-Haideri, Jor bagh, New Delhi bayan samun umarnin shugabanmu Maulana Kalbe Jawad Naqvi mun yanke hukunin daukan nauyinsa. Don haka muna rokon ka amince da bukatarmu, kuma ka bamu dama.” In ji shi.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Zakzaky na fama da cututtukan zuciya ne, kari da hawan jini, lalacewar idanu, cutar gubar karfe da sauran cututtuka da dama a jikinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel