Manajan banki ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wata wasika mai ban mamaki

Manajan banki ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wata wasika mai ban mamaki

'Yan uwa da abokan arzikin wani manaja banki da aka bayyana sunansa da Ibeakanma Onyechere sun shiga halin dimuwa da juyayi bayan samun kabarin cewa ya kashe kansa a unguwar Victoria Island, a jihar Legas.

Onyechere, manajan hulda da jama'a a daya daga cikin fitattun bankunan kasar nan, ya kashe kansa ta hanyar kwankwadar maganin kwarin nan mai karfi 'Sniper' a cikin makon jiya.

Ana zargin cewa manajan bankin ya kashe kansa ne biyo bayan matsananciyar damuwa, musamman irin kalaman da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta 'Facebook da Twitter' a ranar 24 ga watan Yuli, inda ya rubuta cikin harshen turanci cewa, "sannu a hankali hasken sai dusashe wa yake yi."

A wasiyyar da ya bari a cikin wata wasika da ya rubuta kafin mutuwarsa, Onyechere ya bayyana irin soyayyarsa ga matarsa, Cecilia, da kuma diyarsu tare da rokon cewa kar matarsa ta yi kuka saboda mutuwarsa.

DUBA WANNAN: Boko Haram: An yi bikin Sallah a Bama a karo na farko cikin shekaru biyar

"Ina kiran ki da 'sahibata', saboda kaunar da nake yi maki. Ina so ki sani cewa karshen rayuwata a duniya ya zo. Abinda ke damuna ya samu galaba a kai na, ya kuma kawo karshen dukkan wata damu wa ta. Kin yi kuskuren aure na, kin cancanci miji na arziki, ba iri na ba. Kina bukatar farin ciki na gaskiya, kar ki yi kuka saboda mutuwa ta.

"Ki sanar da diyar mu, Chinenyenwa, cewa ina son ta sosai. Ki zauna lafiya da kowa, duk da na san haka abu ne mai wuya. Ki sanar da dangi na cewa ina rokonsu kar wanda ya tsangwame ki bayan mutuwa ta. Kar ki min kuka, addu'arki nake bukata. Sai wata rana masoyiya ta," kamar yadda ya rubuta cikin wasikar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel