Yanzu Yanzu: El-Zakzaky da matarsa sun isa Indiya, za a fara basu kulawa ba tare da bata lokaci ba (hotuna)

Yanzu Yanzu: El-Zakzaky da matarsa sun isa Indiya, za a fara basu kulawa ba tare da bata lokaci ba (hotuna)

Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wanda aka fi sani da Shi’a, da matarsa, Zeenah, su isa Indiya inda su dukka biyun za su yi magani.

Mutanen biyu sun isa Delhi, kasar Indiya da safiyar ranar Talata, 13 ga watan Agusta yan sa’o’i bayan sun bar Najeriya.

Yanzu Yanzu: Shugaban Shi’a El-Zakzaky da matarsa sun isa Indiya, za a fara basu kulawa ba tare da bata lokaci ba (hotuna)
Shugaban Shi’a El-Zakzaky da matarsa sun isa Indiya
Asali: UGC

Wata babbar kotun Kaduna ce ta bayar da belin El-Zakzaky biyo bayan tabarbarewar lafiyarsa.

Rahotanni sun kawo cewa jami’an gwamnatin jihar Kaduna sun yi wa Zakzaky rakiya zuwa yin magani.

Yanzu Yanzu: Shugaban Shi’a El-Zakzaky da matarsa sun isa Indiya, za a fara basu kulawa ba tare da bata lokaci ba (hotuna)
Shugaban Shi’a El-Zakzaky da matarsa sun isa Indiya
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Tafiya Indiya neman magani: Zakzaky ya yada zango a Dubai

A halin da ake ciki, mun ji cewa, Zakzaky tare da mai dakinsa sun yi watsi da tayin fadar shugaban kasa na amfani da daya daga cikin jiragenta wajen aiwatar da wannan baluguro, inda suka yanke shawarar bin jirgin 'yan kasuwa.

Jagoran darikar shi'a na Najeriya ya tafi kasar Indiya cikin jirgin kamfanin Emirates a ranar Litinin kamar yadda kakakin kungiyar IMN, Ibrahim Musa ya bayar da tabbaci a wata hira da manema labarai ta hanyar wayar tarho.

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, kungiyar IMN ta ce abinda ta dade tana gwagwarmaya ya tabbata biyo bayan ficewar jagoranta Zakzaky neman magani zuwa Indiya. Kungiyar ta ce ta jingine duk wata zanga-zanga a sakamakon cikar burinta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel