Komai ya kankama domin shillawar Zakzaky Indiya (Hotuna)
Komai ya kankama domin tafiyar shugaban kungiyar IMN wanda akafi sani da Shi'a, SheikIbrahim El-Zakzaky, kasar Indiya domin jinya biyo bayan belin da kotun jihar Kaduna ta bashi a makon da ya gabata.
Mun kawo muku rahoton cewa an tafi da Sheik Ibrahim Zakzaky birnin tarayya Abuja. El-Zakzaky zai tafi Indiya tare da matarsa Zeenat inda za su nufi Asibitin Medenta dake New Delhi a kasar ta Indiya domin a duba lafiyarsu.
Wata majiyar IMN dake Kaduna ce ta sanar da wakilin Daily Trust wannan labarin inda ta ce, jagoran na IMN yanzu haka yana Abuja tare da jami’an tsaron DSS inda yake jiran tashinsu zuwa Indiya a wani karamin jirgin sama.
A yanzu haka, Sheikh Zakzaky da iyalinsa suna babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja kuma zasu tashi da jirgin Emirates misalin karfe 6 daidai.
Kalli hotunan Zakzaky a Abuja:

Asali: Facebook
KU KARANTA: Jami'ar Bayero dake Kano ta samu lasisin kafa gidan Talabijin

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng