Wanda bai ji bari ba: Saurayi ya murde wuyan budurwarsa a wani gidan holewa

Wanda bai ji bari ba: Saurayi ya murde wuyan budurwarsa a wani gidan holewa

An tsinci gawar wata budurwa mai suna Jessica a wani daki dake cikin wani gidan holewa dake yankin Marogo na unguwar Badagry ta jahar Legas, wanda ake zargin saurayinta ne ya kashe, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito budurwar tare da saurayinta da har yanzu ba’a san ko wanene ba, sun sauka a gidan holewar na Southbound Hotel ne a daren Juma’a, 9 ga watan Agusta.

KU KARANTA: An karrama gwamnan Kaduna da babbar Sarauta a yayin bikin babbar Sallah

Sai dai da yansanda suka isa dakin don ganin gawar Jessica, sun tabbatar da cewa alamu na bayyane sun nuna saurayin nata wanda a yanzu haka ya tsere, shi ne ya kashe Jessica ta hanyar murde mata wuya.

Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa sun hangi Jessica tare da wannan saurayi nata kuma makashinta a dakin da ake shan giya suna kwankwadar barasa. Don haka rundunar Yansanda ta dauki alwashin kamo wannan matashi.

Kaakakin Yansandan jahar Legas, Bala Elkana ne ya bada wannan tabbaci, inda yace: “Alamu daga wuyanta sun nuna ta wahala, don haka muke ganin murde mata wuya a kayi, sa’annan ka jini ta ko ta ina, a yanzu dai mun garzaya da gawarta zuwa dakin bincike.

“Kwamishinan Yansandan jahar Legas, Zubairu Mu’azu ya umarci sashin binciken manyan laifuka su kaddamar da bincike a kan lamarin don gano musabbabin kisan, tare da kamo saurayin nata.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel