Kashin Dankali: FG zata yi wa tsarin raba kudin tarayya garambawul

Kashin Dankali: FG zata yi wa tsarin raba kudin tarayya garambawul

Gwamnatin tarayya ta ce zata kafa wani kwamiti a cikin satin gobe domin ya sake duba tsarin rabon kudin tarayya zuwa gwamnatocin Jihohi da kananan hukumomin kasar nan.

Mista Elias Mbam, shugaban hukumar rabon kudin gwamnatin tarayya (RMAFC), ne ya bayyana hakan ranar Talata, jim kadan bayan karbar wata kyautar iya aiki da kungiyar ma'aikatan Najeriya ta bashi.

A cewar tsarin rabon kudin da ake amfani da shi a halin yanzu, gwamnatin tarayya na karbar kaso 52.68%, jihohi su karbi kaso 26.72, su kuma kananan hukumomi su samu kaso 20%.

Kazalika, ana bawa jihohi masu arzikin man fetur karin kaso 13% na kudin harajin da gwamnati ta karba daga kasuwancin man fetur da sinadarin iskar gas.

An tsara manhajar rabon kudin ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Amma daga baya sai hukumar RMAFC ta fahimci akwai bukatar yi wa manhajar garambawul, lamarin da yasa ta kafa wani kwamiti a shekarar 2013 domin ya yiwa tsohuwar manhajar rabon kudin garambawul. Kwamitin ya tuntubi masana da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimin kasafi da tattalin arziki da na sarrafa haraji.

A shekarar 2014 ne kwamitin ya samar da sabuwar manhajar rabon arzikin gwamnatin.

Sai yanzu bayan shekara biyar hukumar ta sanar da kafa kwamitin da zai duba sabuwar manhajar tare da bayar shawarwari kafin a fara aiki da ita.

Mbam ya kara da cewa RMAFC zata kara zaburar da hukumomin karbar haraji domin su kara zage dantse wajen tara wa gwamnati kudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel