Bayan shekaru 4 da aure, sabuwar amaryar sarkin Kano ta tare

Bayan shekaru 4 da aure, sabuwar amaryar sarkin Kano ta tare

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya karbi tarewar matarsa ta hudu, diyar mai martaba Lamidon Adamawa, Sa'adatu Barkindo Mustapha, shekaru hudu bayan daura aurenta.

An kawo sabuwar amaryar fadar sarkin Kano ne a ranar Asabar kuma za'a gudanar da Budar Kai a ranar Lahadi.

Sabuwar amaryar ta kammala karatunta a wata jami'ar kasar Ingila inda ta tafi karatu bayan aurenta.

Bayan shekaru 4 da aure, sabuwar amaryar sarkin Kano ta tare
Bayan shekaru 4 da aure, sabuwar amaryar sarkin Kano ta tare
Asali: Facebook

KU KARANTA: Dokar hana kiwo: Mun damke makiyaya 81, mun kwace shanaye 3000 - Gwamna jihar Benuwe

Za ku tuna cewa mai marata sarki Sanusi ya auri diyar Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Mustafa, a ranar 25 ga watan Satumba, 2019.

Sa'adatu Barkindo ta auri sarkin Kano tana yar shekara 18 bayan kammala karatun sakandare.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ne wakilin mai martaba sarkin Kano, yayinda tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, ya zama walliyinta kuma ya bada ita.

Wannan itace matar sarkin Kano ta hudu bayan Maryam, Rakiya da Sadiya, diyar marigaryi Ado Bayero.

A bangare guda, A ranar Asabar, Sashen matasan kungiyar yan kabilar Inyamurai, Ohanaeze Ndigbo, sun lashi takobin cewa za su fitittiki makiyaya daga dazaukan dake kananan hukumomi 95 na kasar Igbo.

Shugaban kungiyar, Okechukwu Isiguzoro, ya bayyana cewa sun yanke wannan shawara ne bayan garkuwa da limamin cocin katolika, Paul Offu, da ya faru ranar 1 ga watan Agusta a hanyar Ihe-Agdbudu dake karamar hukumar Agwu na jihar Enugu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel