Tsuntsu daga sama gasashshe: Aliko Dangote zai dauki zakakuran daliban jami’ar Wudil aiki

Tsuntsu daga sama gasashshe: Aliko Dangote zai dauki zakakuran daliban jami’ar Wudil aiki

Hamshakin dan kasuwa, kuma attajirin da ya fi duk wani attajiri arziki a nahiyar Afirka, dan asalin jahar Kano, Alhaji Aliko Dangote ya dauki alkawarin daukan zakakuran daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta jahar Kano aiki a kamfanoninsa.

Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban jami’ar kimiyya da fasaha ta jahar Kano dake Wudil, Farfesa Shehu Alhaji Musa ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace Dangote ya dauki wannan alkawari ne a yayin zaman hukumar gudanarwar jami’ar.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya nada Aliyu Tilde, Ladan Salihu, Aminu gamawa mukamin kwamishinoni

Tsuntsu daga sama gasashshe: Aliko Dangote zai dauki zakakuran daliban jami’ar Wudil aiki
A yayin zaman hukumar jami'ar Wudil
Asali: Facebook

Farfesa Shehu ya bayyana cewa Dangote zai dauki daliban jami’ar da suka kammala digiri da maki mafi daraja (First Class) da mabi dashi (2:1) daga fannonin aikin injiniya, kimiyyar zane zane, da kuma noma.

Bugu da kari attajirin dan kasuwan ya yi alkawarin janyo babban layin wutar lantarki zuwa jami’ar domin samar da isashshen wutar lantarki a jami’ar don saukaka karatun dalibai da sauran ayyukan jami’ar.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan zama akwai Aliko Dangote kansa, tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, A.B Mahmud SAN, Farfesa Shehu Alhaji Musa da sauran manyan jami’an jami’ar.

A wani labarin kuma, hukumar kula da jin dadin alhazai ta Najeriya ta nemi hukumar JAMB ta bata sunayen dalibai Musulmai da suka fi samun sakamako mai kyau a jarabawar JAMB domin ta kaisu aikin Hajjin bana.

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da haka a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, inda yace baya ga hukumadr Hajji, akwai wasu bankuna guda da suka nemi daukan nauyin karatun dalibai 100 da suka fi samun maki mai daraja, a manyan makarantun Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel