Rikicin kabilanci: Gwamnatin jahar taraba ta sanya dokar hana shige da fice

Rikicin kabilanci: Gwamnatin jahar taraba ta sanya dokar hana shige da fice

Gwamnatin jahar Taraba ta sanar da kakaba dokar tabaci da ta hana shige da fice a garin Takum na jahar Taraba sakamakon rikicin kabilanci tsakanin kabilun Jikunawa da Tibabe, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jukunawa sun kaddamar da harin martani ne a kan kabilun Tibi dake garin Wukari, Jukunawa sun kaddamar da wannan harin ne bayan tsintar gawar wani dan uwansu a gonarsa, wanda suke zargin Tibabe ne suka kasheshi.

KU KARANTA: Allah ya tona asirin wasu yan bindiga, an kama alburusai 10,000 a hannunsu

A yayin harin da Jukunawa suka kai sun kashe jama’an kabilun Tibi da dama, tare da kona gidajensu, wanda hakan tasa sauran tibaben da suke rage a garin suka fice domin tsira da ransu.

Amma a yanzu wani mazaunin garin, Malam Musa Muhammad ya bayyana cewa an samu kwanciyar hankali a garin, kowa na zaune a cikin gida, yayin da dakarun rundunar Sojin Najeriya suke gudanar da sintiri a kan tituna.

Sai dai a nasa jawabin, kaakakin rundunar Yansandan jahar Taraba, DSP David Misal ya bayyana cewa zuwa yanzu mutum daya aka kashe, amma a yanzu komai ya lafa kuma hankali ya kwanta.

Garin Takum shine mahaifar tsohon babban Sojan Najeriya, Janar T.Y Danjuma da kuma gwamnan jahar, Darius Ishaku, amma garin ya dade yana fama da matsalolin da suka shafi garkuwa da mutane da kuma rikicin kabilanci tsakanin Tibabe da Jukunawa.

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Oyo ta sanar da kama wasu yan bindiga guda hudu da suka shahara wajen safarar makamai da alburusai ga kungiyoyin yan fashi da makami, da masu garkuwa da mutane a jahar.

Yansandan sun kama mutanen ne dauke da alburusai guda 10,000, kamar yadda kwamishinan Yansandan jahar, Shina Olukolu ya bayyana, inda yace a ranar 23 ga watan Yuli suka kama mutanen da misalin karfe 2 na dare a unguwar Oke-Bola na garin Ibadan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel